Bayan Fiye da Shekara 1, Gwamnatin Kano Ta Waiwayi Iyalan Mafarautan da Aka Kashe a Uromi

Bayan Fiye da Shekara 1, Gwamnatin Kano Ta Waiwayi Iyalan Mafarautan da Aka Kashe a Uromi

  • Gwamnatin jihar Kano ta cika alkawarin da ta daukarwa iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi ta jihar Edo
  • Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na Kano ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen raba tallafi ga mutanen
  • Ibrahim Abdullahi Waiya ya kuma bayyana cewa ana kokarin tabbatar da cewa gwamnatin jihar Edo ta biya diyyar da ta yi alkawari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta cika alkawarin da ta daukarwa iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi.

Gwamnatin Kano ta raba N7.4m ga iyalai da kuma waɗanda suka tsira daga harin da aka kai wa mafarautan a Uromi da ke jihar Edo a shekarar 2025.

Gwamnatin Kano ta ba da tallafi ga iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce an gabatar da wannan tallafin kuɗi ne a faɗar sarkin Bunkure da ke ƙaramar hukumar Bunkure a jihar Kano a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta bullo da shirin ba da rancen kudin hawa jirgin sama a Najeriya

Gwamnatin Abba ta cika alkawari

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ne ya wakilci Gwamna Abba a wajen raba kudin, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Ya bayyana cewa wannan matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage raɗaɗin wahalhalun da iyalai da waɗanda suka tsira daga wannan mummunan lamari ke fuskanta.

Ibrahim Waiya ya bayyana cewa an ba kowanne daga cikin iyalai 16 na waɗanda suka rasa rayukansu N300,000, yayin da mutane 13 da suka tsira aka ba kowannensu N200,000.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa an ba da kayan abinci da suka haɗa da buhunan shinkafa guda biyu ga kowane mutum.

Ya bayyana cewa wannan tallafin ya yi daidai da alƙawarin da gwamnan ya ɗauka a baya lokacin da ya ziyarci al'ummar don yi musu ta'aziyya jim kaɗan bayan harin.

Abba ya yi tsammanin an cika alkawari

A cewarsa, gwamnan ya yi tsammanin an riga an cika wannan alƙawarin, amma bayan ya gano akasin haka, sai ya bayar da umarnin ɗaukar mataki cikin gaggawa don tabbatar da tallafin ya isa ga waɗanda ya kamata ya kai wa.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati ta yi ganawar sirri da Sarki gabanin sanar da hawan Sallah a Kano

"Muna nan ne don cika alƙawarin da Mai Girma Gwamna ya ɗauka lokacin da ya ziyarta tare da nuna alhini ga iyalai da waɗanda kisan gillar Uromi ya shafa."

- Ibrahim Waiya

Ya bayyana lamarin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 tare da jikkata wasu 13, a matsayin babban bala'i na ƙasa, inda ya bayyana cewa wasu fusatattun mutane ne suka kai wa waɗanda abin ya shafa hari yayin da suke kan hanyar dawowa Arewa.

Gwamnatin Kano ta cika alkawari
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ana shirin biyan iyalan mafarauta diyya

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa an biya diyyar da gwamnatin jihar Edo ta yi alƙawari, inda ya bayyana cewa tuni aka buɗe wani asusun banki na musamman don wannan manufa.

Ya nuna kyakkyawan fata cewa nan ba da jimawa ba za a saki diyyar, inda ya ƙara da cewa gwamnatocin jihohin biyu sun jajirce wajen ganin an yi adalci tare da ba wa waɗanda abin ya shafa tallafi.

Ibrahim Waiya ya buƙaci iyalan da abin ya shafa da su yi haƙuri, yana mai tabbatar musu da ci gaba da samun goyon bayan gwamnati.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Sanusi II ya jagoranci Sallar Idi a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Idi a filin Idi na Kofar Mata domin kammala watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.

Muhammadu Sanusi II ya fito daga fadar Gidan Rumfa a kafa domin gudanar da Hawan Idi, sakamakon dokar gwamnati ta hana hawan doki.

Sarkin ya isa ta hanyoyin da aka tsara tare da jagorantar dubban masu ibada, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng