Gwamnatin Tarayya Ta Bullo da Shirin ba da Rancen Kudin Hawa Jirgin Sama a Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Bullo da Shirin ba da Rancen Kudin Hawa Jirgin Sama a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta bullo da wani shiri na ba da lamunin sayen tikitin jirgin sama domin saukakawa mutane zirga-zirga a cikin gida
  • Hukumar CrediCorp ta ce wannan shiri zai rage wa 'yan Najeriya nauyin biyan kudin tikitin jirgi lokaci guda, wanda ke kawo cikas ga mutane
  • CrediCorp ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa damar samun lamuni mai inganci ga ‘yan Najeriya domin inganta rayuwarsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta bullo da wani shiri domin tallafawa 'yan Najeriya wajen zirga-zirga a jiragen sama.

Gwamnatin ta ta ƙaddamar da sabon tsarin mai suna “Fly Now, Pay Later” domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin tafiye-tafiyen jirgin sama cikin sauƙi.

Jirgin sama.
Jirgin sama yayin da yake tsakiyar tafiya a sararin samaniya Hoto: Picture Alliance
Source: Getty Images

A wani sako da Hukumar ba da Lamuni ga Mabukata ta Najeriya (CrediCorp) ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa shirin zai bai wa waɗanda suka cancanta damar samun bashin tikitin jirgi na cikin gida sannan su biya kuɗin a hankali.

Kara karanta wannan

NRC ta tsara zirga zirgar jiragen kasa na musamman a lokacin laramar Sallah a Najeriya

Yadda tsarin bashin zai gudana

Hukumar ta ce an samar da wannan tsari ne domin rage nauyin biyan kuɗin tikiti gaba ɗaya, wanda sau da yawa ke hana mutane yin tafiya a jiragen sama domin biyan bukatunsu a kan lokaci.

Ta kuma bayyana cewa hukumar ta haɗa hannu da kamfanin MyVisaro da Alert Microfinance Bank wajen aiwatar da shirin.

Masu sha’awar cun gajiyar wannan shirin na lamuni za su iya shiga shafin visaro.ng domin yin rajista da ajiyar tikitin jirgi zuwa kowane birni a Najeriya.

Bincike ya nuna cewa dole ne mutum ya fara da biyan kashi 30 cikin 100 na kuɗin tafiya, sannan a raba sauran kuɗin zuwa kashi uku da za a biya a cikin watanni uku.

Dalilin ƙaddamar da shirin

Wannan shiri na zuwa ne a daidai lokacin da farashin tikitin jirgin sama a cikin gida ya yi tashin gwauron zabo, lamarin da ya jefa matafiya da dama cikin matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

CrediCorp ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa damar samun lamuni mai inganci ga ‘yan Najeriya domin inganta rayuwarsu, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na daga hannu kafin ya shiga jirgin sama a Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

A cikin ‘yan watannin baya-bayan nan, hukumar ta ƙaddamar da shirye-shirye da dama da suka shafi matasa, masu ritaya da kuma masu sha’awar mallakar motoci.

A watan Disambar 2024, CrediCorp ta haɗa gwiwa da Hukumar NADDC wajen ƙaddamar da asusun lamuni na Naira biliyan 20 domin bai wa ‘yan Najeriya damar sayen motocin da aka ƙera a cikin gida.

Jirgi dauke da sanata ya samu matsala

Kun ji cewa Sanatan Taraba ta Kudu, David Jimkuta da wasu jiga-jigan APC sun tsallake rijiya da baya da suka bi wani jirgin sama a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman da sanatan ke ciki ya samu matsalar fasaha jim kadan bayan tashinsa, lamarin da ya tilasta masa saukar gaggawa.

Daga cikin wadanda ke cikin jirgin akwai shugaban cocin Christian Reformed ta Najeriya, Magaji Jirape da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Istifanus Gbana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262