NRC Ta Tsara Zirga Zirgar Jiragen Kasa na Musamman a Lokacin Karamar Sallah a Najeriya

NRC Ta Tsara Zirga Zirgar Jiragen Kasa na Musamman a Lokacin Karamar Sallah a Najeriya

  • Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana shirinta na kara yawan jirage a kan manyan layukan dogo lokacin bukukuwan Sallah
  • NRC ta bayyana cewa za a ƙara yawan zirga-zirgar jiragen kasa a hanyoyin Lagos–Ibadan da Abuja–Kaduna domin saukakawa al'umma
  • Gwamnatin Osun za ta samar da jirgin kyauta ga ‘yan jiharta domin tallafa masu a wannan lokaci na shagulgulan karamar Sallah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya, – Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta sanar da ƙarin zirga-zirgar jiragen ƙasa na musamman a manyan hanyoyi domin sauƙaƙa tafiya yayin bukukuwan karamar Sallah

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa wannan shiri na wucin gadi ne.

Jirgin kasa.
Daya daga cikin jiragen kasa da ke zirga-zirga a Najeriya Hoto: @NRCNigeria
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta tattaro cewa hukumar NRC ta tsara wannan shiri ne domin samar da sufuri mai sauƙi, aminci da inganci yayin da ake sa ran yawaitar fasinjoji a lokacin shagulgulan sallah.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati ta yi ganawar sirri da Sarki gabanin sanar da hawan Sallah a Kano

Karin jirage kasa a manyan layukan dogo

Hukumar ta ce za a ƙara jiragen kasa a manyan hanyoyi kamar Lagos–Ibadan da Abuja–Kaduna domin biyan bukatar fasinjoji.

A kan hanyar Lagos–Ibadan, za a gudanar da tafiye-tafiye uku na musamman a ranar 19 ga Maris, 2026 daga kowane bangare.

Jiragen da za su tashi daga tashar Mobolaji Johnson da ke Ebute Metta a Lagos za su fara ne da karfe 7:40 na safe, 1:40 na rana da kuma 4:00 na yamma.

A daya bangaren kuma, jirage daga tashar Obafemi Awolowo da ke Moniya a Ibadan za su tashi da karfe 8:00 na safe, 10:50 na safe da kuma 4:30 na yamma.

A hanyar Abuja–Kaduna kuwa, NRC ta bayyana cewa za ta gudanar da tafiye-tafiye biyu a ranar 19 ga Maris, sannan daga ranar 20 zuwa 23 ga Maris, 2026 za a rika yin tafiye-tafiye uku a kullum domin bai wa fasinjoji damar zabi cikin sauƙi.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Jirgin kyauta da aka samar a Osun

Hukumar ta kuma bayyana haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Osun wajen gudanar da jirgin “Imole Special Train”, wanda zai dauki ‘yan asalin jihar daga tashar Iddo da ke Lagos zuwa Osogbo kyauta.

An bayyana cewa gwamnatin Osun ce ke daukar nauyin wannan shiri gaba daya, yayin da NRC ke samar da jirage, fasaha da kuma tafiyar da ayyukan. Wannan mataki na daga cikin kokarin tallafa wa jama’a a lokacin bukukuwan Sallah.

Gwamna Seyi Makinde.
Jirgin kasa da gwamnan jihar Osun, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: UGC

Hukumar NRC ta tabbatar wa fasinjoji cewa za ta ci gaba da samar da sufuri mai aminci da inganci a dukkan hanyoyinta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Za a fadada layin dogo zuwa jihohin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa hukumar NRC ta sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta kaddamar da sabuwar taswirar layin dogo da zai zagaye jihohin Najeriya.

Taswirar za ta tabbatar da cewa dukkan jihohi 36 na kasar da babban birnin tarayya Abuja sun samu layin dogo kai tsaye.

Shugaban NRC, Kayode Opeifa, ya bayyana cewa sabuwar taswirar za ta bai wa kowace jiha damar shiga cikin tsarin layin dogon kasa ba tare da biyan kudin aikin samar da jiragen kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262