Malamin Musulunci Ya Bijirewa Sarkin Musulmi, zai Yi Sallar Azumi a Yau Alhamis

Malamin Musulunci Ya Bijirewa Sarkin Musulmi, zai Yi Sallar Azumi a Yau Alhamis

  • Malamin Musulunci, Shekh Musa Ayyuba Lukuwa ya sanar da cewa zai jagoranci sallar Idi a yau Alhamis, 19 ga watan Maris 2026
  • Malamin ya bayyana haka ne yayin wani wa'azi da ya yi cikin dare bayan mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa ba aga wata ba
  • Sheikh Lukuwa ya dauki wannan matsaya ne duk da cewa mafi yawancin malamai za su bi umarnin sarkin Musulmi a fadin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya sanar da cewa sun kammala azumin watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Maris 2026.

Biyo bayan haka malamin ya sanar da cewa zai fito ya yi sallar Idi domin a cewarsa idan Ramadan ya kare sai bukukuwan sallah.

Kara karanta wannan

'Za a cika azumi 30,' An gano ba za a ga watan Shawwal ba a Najeriya

Masu idi da Sheikh Ayuba Lukuwa
Sheikh Musa Lukuwa da ya ce zai yi idi a yau. Hoto: Sheikh Ayyuba Musa Lukuwa Sokoto|Getty Images
Source: Facebook

Sheikh Lukuwa ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook jim kadan bayan mai alfarma sarkin Musulmi ya sanar da cewa ba a ga wata ba.

Sheikh Lukuwa zai yi sallar azumi

Sheikh Lukuwa ya bayyana cewa azumin Ramadan na 1447 ya kare da ya cika kwana 29 a lissafin da suka yi, saboda haka za su yi sallah a yau Alhamis.

Malamin ya bayyana cewa an sanar da ganin wata a kasar Nijar, kuma kasar ta fi kusa da Najeriya sama da Saudiyya kuma ta fi kusa da Sokoto sama da Legas.

A daren Laraba ya bayyana cewa:

"Muna tabbatar muku in shaa Allah gobe (Alhamis) za mu yi sallar idi, azumin mu ya kare, gobe 1 ga Shawwal."

Maganar sanar da watan Sultan

Sheikh Lukuwa ya kara da cewa ba su adawa da sanarwar ganin wata da Sarkin Musulmi ya ke yi a Najeriya domin suna masa biyayya.

Kara karanta wannan

Da gaske Gwamna Abba ya ce Sanusi II ba zai yi hawan sallah a Kano ba?

Ya ce ana samun sabani da su ne kawai idan aka ga wata amma ba a sanar ba, inda ya kara da cewa suna yi wa shugabanni biyayya a duk lokacin da aka ce an ga wata.

Mai alfarma Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi yayin wani jawabi. Hoto: Sultane Council Media Unit
Source: Facebook

Sheikh Lukuwa ya yi martani ga masu cewa sarkin Musulmi ne kawai ke da ikon sanar da al'umma an ga wata ko ba a gani ba, yana mai cewa hakan ba ya cikin tsarin Shari'a.

Malamin ya kalubalanci masu irin fahimtar da su sanar da shi aya ko hadisi da suka ce ga wanda zai sanar da ganin wata a Shari'a.

Za a yi azumi 30 a Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai sharh game da yanayi da sararin samaniya, Adamu Ya'u da aka fi sani da Dan America ya yi hasashen cewa azumi 30 za a yi a bana.

Dan America ya bayyana cewa ba yadda za a ga wata a kasashen da suka hada da Najeriya, Nijar da Saudiyya a yammacin ranar Laraba, 18 ga watan Maris, 2026.

A bayanan da ya yi, masanin ya sanar da lokutan da rana za ta fadi a birnin Makkah na Saudiyya, birnin Jimeta na Najeriya da kuma birnin Yamai na kasar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng