29 Ko 30: Malamin Addini Ya Riga Sarkin Musulmi, Ya Sanar da Ranar Karamar Sallah a Najeriya
- Azumin Ramadan na shekarar 2026 yana gab da ƙarewa, kuma Musulmi a faɗin duniya suna shirin gudanar da bikin karamar Sallah (Eid al-Fitr)
- Yayin da Ramadan ke zuwa ƙarshe, ranar gudanar da bikin ƙaramar Sallah ta zama abin muhawara yayin da ƙasashe da dama suka sanar da matakan neman jinjirin wata
- Mudir Markaz Sheikh Habibullah Adam ya sanar da tsawon azumin Ramadan na 2026 da kuma lokacin da za a gudanar da bikin ƙaramar Sallah a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Habibullah Adam, ya yi magana kan ranar da za a kammala azumin watan Ramadan.
Sheikh Habibullah Adam ya bayyana cewa azumin Ramadan na 2026 zai cika kwanaki 30 cif-cif.

Source: Facebook
Yaushe malamin ya ce za a yi Sallah?
Babban malamin addinin Musuluncin ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyon da aka sanya a shafin Facebook.
Malamin addinin ya yi wannan sanarwar ne a lokacin shirin daren Lailatul Qadr na cibiyar, wanda aka gudanar a daren Lahadi zuwa safiyar Litinin, 15 da 16 ga Maris 2026.
Hakazalika, ya bayyana za a gudanar da bikin karamar Sallah a ranar Juma’a, 20 ga watan Maris 2026.
Menene watan Ramadan?
Ramadan shi ne wata na tara a cikin jerin watannin Musulunci, kuma ana ɗaukar sa a matsayin wata mai alfarma.
Bisa al’ada, azumi yana farawa ne tun kafin asuba, inda kafin nan ake cin abinci mara nauyi da ake kira 'sahur', sannan ya kare lokacin faɗuwar rana, wanda ake kira buda baki watau 'Iftar'.
Tsakanin waɗannan lokuta biyu na cin abinci, Musulmin da ke azumi ba za su ci komai ba, koda kuwa ruwa ne.
Azumin Ramadan wajibi ne ga dukkan Musulmi a faɗin duniya, kuma lokaci ne da masu imani ke ayyuka na kwarai tare da nisantar ayyuka marasa kyau.
Martanin da aka yi wa Sheikh Habib
Bidiyon wanda aka wallafa a shafin Facebook na Markaz, ya fara janyo martani daga ‘yan Najeriya.
Ga wasu daga cikin kalaman nasu:
Ajiboye Thomas ya taya Musulmi murna tun kafin lokacin:
"Yayi kyau, Babanmu na Musulunci, ina maka barka da Sallah."

Source: Facebook
Proff Abdullahi ya ba da ƙarin bayani kan ganin wata:
"Me ya sa ranar Sallah ta zama ranar Juma’a? Ana sa ran ranar ƙaramar Sallah za ta faɗo ne a ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026, amma ainihin ranar na iya sauyawa dangane da ganin jinjirin watan da ke nuna farkon watan Shawwal, watan Musulunci da ke biyo bayan Ramadan."
"Ganin sabon jinjirin wata ne ke tabbatar da farkon watan Shawwal da ƙaramar Sallah. Ana iya tabbatar da ganin wata ta hanyar kwamitocin gida, sanarwar masallatai, ko lissafin ilimin taurari. Ƙasashe daban-daban na iya sanar da ranar Sallah a ranaku mabanbanta dangane da ganin wata a yankunansu."
Oke Moses Adewale ya jinjina wa malamin:
"Ina alfahari da kai, Baba na Agege."
Ba a ga wata ba a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukunta a Saudiyya sun fitar da sanarwa kan lokacin gudanar da bukukuwan kararmar Sallah na shekarar 2026.
Saudiyya ta tabbatar da cewa ba a samu sahiihin rahoton ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1447AH ba a ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan, wanda ya zo daidai da 18 ga watan Maris, 2026.
masarautar Saudiyya ta bayyana cewa musulmi za su cika azumi 30 cif a wannan shekara, tare da ayyana ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranar karamar Sallah.
Asali: Legit.ng


