Ana Shirin Sallah, Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Yakin Iran da Amurka

Ana Shirin Sallah, Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Yakin Iran da Amurka

  • Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bukaci kowane Musulmi ya fito duba wata a yau Laraba, 18 ga Maris 2026
  • NSCIA da ke aiki karkashin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III tayi matsaya game da yakin da ake da Iran
  • Majalisar ta kuma bukaci al'ummar Musulmi su shirya fitar da zakkar fidda kai yayin da ake shirin kammala azumin watan Ramadan na bana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya yi maganar fita duba wata a wata sanarwa da ya fitar.

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta yi kira ga kowane Musulmi ya fita duba wata da yammacin yau Laraba.

Kara karanta wannan

Azumi ya zo karshe, Sarkin Musulmi ya fitar sanarwa kan ranar karamar Sallah a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi yana jawabi a wani taro a Najeriya. Hoto: Sultanate Council Media Team
Source: Facebook

NSCIA ta fitar da matsayarta game da yakin da Amurka ta hada kai da Isra'ila ta kaddamar kan Iran a wani sako da ta wallafa a shafinta a intanet.

Maganar duba wata a Najeriya

Majalisar NSCIA ta bukaci kowa da kowa ya fita duba wata yayin da al'umar Musulmi ke shirin kammala azumin watan Ramadan.

Ta ce:

"Muna kira ga dukkan Musulmi a Najeriya da su fito su hada kai wajen neman jinjirin a ranar Laraba, 29 ga Ramadan 1447AH, wanda ya yi daidai da 18 ga Maris 2026.

Game da zakkar fidda kai, Sarkin Musulmi ya ce:

"Don haka, ana kira ga dukkan Musulmi da su cika wajibansu na addini, ciki har da fitar da zakkar fidda kai ga iyalansu da wadanda suke karkashinsu."

Magana kan yakin Iran da Amurka

Majalisar NSCIA ta ce ta shiga damuwa kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar 28 ga Fabrairu 2026.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Ta ce:

"A bayyane yake cewa hare-haren sun sabawa mataki na 2(4) na kundin tsarin majalisar dinkin duniya."
"Baya ga kai hari da kashe jagoran koli na kasar, Ayatollah Ali Khamenei, da wasu daga cikin ‘yan uwansa, hare-haren sun kuma jawo mutuwar kusan ‘yan makaranta 200 a Kudancin kasar."

Majalisar ta kara da cewa babu shakka Amurka da Isra’ila su ne suka fara yakin, kuma dokokin kasa da kasa sun bai wa kowace mamba ta majalisar dinkin duniya damar kare kanta idan an kai mata hari.

Sabon jagoran addini na Iran a wani taro
Mojtaba Khamenei a wani taro kafin zama jagoran Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwa ta ce:

"Sai dai, in ba ga wadanda ke cikin jahilci ko masu kyamar Musulunci ba, abin da ke bayyane shi ne kiyayyar Musulunci da kuma yunkurin manyan kasashe na murkushe Musulmi."

Ta kara da cewa Irin wannan tsari ne aka yi amfani da shi wajen rusa kasashe Musulmi da dama kamar Libya, Syria, Afghanistan, Somalia, Sudan, Yemen da Iraq, ta hanyar tayar da rikici, kashe shugabanni, rusa gwamnatoci da wargaza al’umma.

Kara karanta wannan

Za a yi makoki a Israi'ila, Trump na yaki da Iran, an kai hari kan yahudawa a Amurka

Martani ga majalisar dinkin duniya

Sarkin Musulmi ya ce abin takaici ne yadda majalisar dinkin duniya ta yi Allah-wadai da Iran kawai kan abin da ya shafi zirga-zirga a mashigar Hormuz, ba tare da yin Allah-wadai da kasashen da suka fara kai mata hari ba.

Ta kara da cewa:

"Muna kira ga kasashen duniya su nuna jarumta wajen fadin gaskiya domin hana kowace kasa kai hari ba bisa ka’ida ba kan wata kasa mai cin gashin kanta."

An ce ba za a ga wata ba

A wani labarin, kun ji cewa masu sharhi kan ganin wata sun fara magana game da fita duba jinjirin wata yayin da ake rana ta 29 ga Ramadan.

Adamu Ya'u da aka fi sani da Dan America da ke sharhi kan yanayin sararin samaniya ya bayyana cewa ba zai yiwu a ga wata ba a yau Laraba.

Dan America ya fadi lokutan da wata zai fito a fito a Najeriya, Jamhuriyar Nijar da Saudiyya a wani hasashen da ya fitar game da kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng