'Za a Cika Azumi 30,' An Gano ba za a ga Watan Shawwal ba a Najeriya
- Yayin da mai alfarma Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar fita duba watan Shawwal a Najeriya, masana taurari sun fara sharhi game da batun
- Wani masanin taurari, Adamu Yau da aka fi sani da Dan America, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ga watan Shawwal ba a yau Laraba
- Adamu Dan America ya yi karin haske game da yadda wata zai fito a yau a kasashe da dama ciki harda Saudiyya, Najeriya da Jumhuriyar Nijar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Masana taurari sun fara bayani game da duba watan Shawwal da za a fara a yau Laraba, 18 ga watan Maris yayin da aka yi azumi 29.
Mai sharhi kan ganin wata, Adamu Ya'u da aka sani da Dan America ya bayyana cewa ba yadda za a ga wata da yammacin yau Laraba.

Source: Facebook
Legit Hausa ta rahoto cewa Dan America ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook yana sharhi kan duba wata.
Yadda wata zai fito a Saudiyya
Adamu Ya'u ya bayyana cewa ko na'ura 10,000 aka yi amfani da su ba za a ga wata a Saudiyya ba ranar 29 ga Ramadan a ranar Laraba.
Ya ce wata zai kasance yana da sauran haske a ranar 29 bayan faduwar rana, inda ya ce wata zai fadi da karfe 6:03 na yamma rana kuma 6:31 na yamma a garin Makkah.
Bisa ilimin kimiyya, Dan America ya ce ba za a ga wata ba bayan faduwar rana. Saboda haka ya ce yana da tabbacin ba za a ga wata ba a Saudiyya.
Maganar ganin wata a Najeriya
A Najeriya kuma, Dan America ya bayyana cewa wata zai fadi karfe 5:58 rana za ta fadi 6:21 a karamar hukumar Jimeta a jihar Adamawa.
Ya ce akwai minti 23 a tsananisu a Jimeta, inda ya kara da cewa haka abin ya ke a sauran jihohi, za a samu bambancin minti ɗaya ko biyu ne kawai.

Source: Facebook
Dan America ya ce ko wasu sun ce sun ga wata ba za a yarda ba saboda kwata-kwata ba zai yiwu a kalli watan ba bisa hasashen yanayi.
Ya ce:
"Ko wasu sun ce sun ga wata ba za a yarda ba."
Za a cika azumi 30 a bana
Dan America ya bayyana cewa a Nijar ma ba za a yarda da labarin ganin wata ba domin a Yamai da karfe 6:40 wata zai fadi, yanayin da ba zai sa a ga wata ba.
Ya bayyana cewa saboda haka dole a cika azumi 30 a bana, domin wasu haske suke hangowa ko tauraron dan Adam su dauka wata ne.
Za a fita duba wata a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya umarci 'yan Najeriya su fita duba watan Shawwal a yau Laraba, 29 ga Ramadan 1447.
An bayyana cewa duk wanda ya ga wata ya sanar da masarauta mafi kusa da shi ko kuma ya tuntubi lambobin da aka tanada.
Idan ba a samu labarin ganin wata ba a yammacin 29 ga Ramadan, mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa za a cika azumi 30.
Asali: Legit.ng

