Hankula Sun Tashi bayan Fashewar Bama Bamai a Maiduguri Ana cikin Shan Ruwa

Hankula Sun Tashi bayan Fashewar Bama Bamai a Maiduguri Ana cikin Shan Ruwa

  • An samu fashewar wasu bama-bamai a babban birnin Maiduguri na jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Fashe-fashen sun auku ne yayin da al'ummar Musulmi suke gudanar da buda baki yayin da ake ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan
  • Kararrakin fashe-fashen da aka ji a wasu wurare biyu na babban birnin sun sanya mutane sun shiga cikin firgici tare da tsorata

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Mazauna birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun shiga cikin firgici a yammacin ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2027.

An shiga firgicin ne biyo bayan ƙararrakin fashe-fashe da aka ji a wurare da dama waɗanda suka tsorata mutane.

Bama-bamai sun tashi a birnin Maiduguri
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa abubuwan fashewa a sassa daban-daban na birnin.

Kara karanta wannan

Bukukuwan Sallah: Jerin gwamnonin Arewa 5 da za su biya albashin Maris da wuri

An tayar da bama-bamai a Maiduguri

Ƙofar asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH), shatale-shatalen hanyar Monday Market da yankin El-Kanemi su ne wuraren da fashe-fashen suka shafa.

An bayar da rahoton jin fashewar farko ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, jim kaɗan bayan al'ummar Musulmi sun yi buɗe baki.

Sojoji sun gwabza da 'yan Boko Haram

Ba a tabbatar da ko an samu asarar rayuka ba sakamakon wannan lamari wanda ya faru sa'o'i kaɗan bayan 'yan ta'adda sun kai hari wani sansanin soji a Ajilari wanda yake wani yanki a bayan garin Maiduguri.

'Yan ta'addan sun kona sansanin tare da yin awon gaba da motar sintiri ta sojoji.

Sai dai kuma, dakarun sojin sun yi nasarar dakile harin tare da kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan, yayin da da dama daga cikinsu suka tsere daga wurin dauke da raunukan harbin bindiga.

Zulum ya yi Allah wadai da fashewar bam

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da kakkausan harshe game da fashe-fashen da suka auku a wasu sassa na birnin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Kasashe 5 da za su iya shiga cikin yakin Amurka, Isra'ila da Iran

Zulum, wanda a halin yanzu yake ƙasar Saudiyya don gudanar da aikin Umrah, ya yi Allah wadai da harin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Dauda Iliya, ya sanya a shafinsa na Facebook.

An tayar da bama-bamai a Maiduguri
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

Gwamna Zulum ya yi kiran da a ƙara sa ido da kuma tsananta matakan tsaro, musamman a wuraren ibada, yayin da lokacin bukukuwan sallah ke gabatowa.

“Ina matuƙar baƙin ciki da fashe-fashen da suka faru a wasu sassa na birnin Maiduguri a yammacin Litinin."
"Tunanina da addu'o'ina suna tare da iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma waɗanda suka ji rauni sakamakon fashewar. Wannan aikin abin Allah-wadai ne, rashin tausayi ne, kuma ya saɓa wa addini."
"Wannan ƙaruwar hare-hare da aka samu ba ya rasa nasaba da zafafa ayyukan sojoji da ake yi a dajin Sambisa da sauran maboyar 'yan ta'adda.”

- Gwamna Babagana Umara Zulum

'Yan Boko Haram sun kashe kwamandan sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa mayakan kungiyar Boko Haram dauke da makamai sun kai wani hari kan sansanin sojoji a jihar Borno.

'Yan ta'addan na Boko Haram sun kashe babban kwamandan rundunar (CO) da wasu jami’an sojojin Najeriya yayin harin da suka kai.

Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun fatattaki dakarun sojoji daga sansanin, suka ƙona motoci tare da kwashe makamai da albarusai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng