Jirgin Kasan Abuja Kaduna Dauke da Fasinjoji Ya Gamu da Hatsari, an Samu Bayanai
- Jirgin kasa da ke dauke da fasinjoji a kan hanyar Abuja-Kaduna ya gamu da hatsari a ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2026
- Fasinjoji da dama sun jikkata sakamakon hadarin wanda ya auku lokacin da jirgin yake tsaka da tafiya a kan hanyar
- Hukumar NRC ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda shugabanta ya bayyana matakan gaggawa da suka dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fasinjoji da dama sun ji raunuka bayan da wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya kauce daga layinsa.
Jirgin kasan ya kauce daga kan layinsa ne biyo bayan wani karo da ya faru a kan hanyar.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne kusa da Asham a kan saƙon layin dogon da ya haɗa Abuja da Kaduna, wanda ya janyo fargaba a tsakanin fasinjojin da ke cikin jirgin.

Kara karanta wannan
"Da na fuskanci kaskanci," Sanusi II ya tuna lokacin da aka cire shi daga sarkin Kano
Jirgin kadan Kaduna-Abuja ya yi hatsari
Shugaban hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa an tura jami’an agajin gaggawa zuwa wurin nan take bayan samun rahoton kaucewar jirgin daga layinsa.
Bisa binciken farko, an gano jirgin ya kauce daga layin ne bayan ya yi karo da wani abu a kan hanyar.
Jami’ai ba su bayar da cikakken bayani ba tukuna game da ainihin yadda karon ya faru ko kuma yanayin abin da ya tare hanyar.
Fasinjoji sun samu raunuka
An bayar da rahoton cewa fasinjoji da dama sun samu raunuka mabanbanta yayin lamarin. An kwashe su zuwa wani asibiti da ke tashar jirgin kasa ta Idu inda a halin yanzu suke karɓar magani.
Hukumomi sun bayyana cewa ba a samu rahoton rasa rai ba zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoto.
Bayanai daga shaidun gani da ido da bidiyoyin da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna taragon jirgin da suka lalace da kuma ma'aikatan layin dogo suna duba jirgin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan
Iran: An harba makamai filin jirgin da Amurka ke aiki da shi, bakin hayaki ya tashi
An kuma ga fasinjojin da suka maƙale sun taru kusa da layin dogon bayan sun fito lafiya, yayin da jami'an ceto ke gudanar da ayyukan kwashe mutane.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Hukumar NRC ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar yau Litinin, 16 ga watan Maris 2026, kusa da Asham.

Source: Original
Wasu fasinjojin sun ji raunuka inda aka kula da su cikin gaggawa tare da kai su asibiti mafi kusa don samun ingantacciyar kulawar likita. Ba a samu asarar rai ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
"An dauki matakan agajin gaggawa nan take, kuma an tura ƙungiyoyin ƙwararru na fasaha zuwa wurin."
"Hukumar SIB ma tana wurin don gudanar da gagarumin bincike kan lamarin daidai da tsarin tsaro da aka shimfiɗa.”
- Kayode Opeifa
Jirgin sojojin Najeriya ya yi hadari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin saman rundunar sojojin sama ta Najeriya ya gamu da hatsari a jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin yakin sojojin ya fado kasa tare da kamawa da wuta a kusa da Karabonde, cikin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Matukan jirgin biyu sun tsira bayan sun yi amfani da rigar sauka ta gaggawa kafin jirgin ya rikito ya fadi kasa.
Asali: Legit.ng