Shugaban Najeriya zai Ziyarci UK Karon Farko a Shekaru 37, An Gano Shirin Kunyata Tinubu
- Gwamnatin Tarayya ta ce akwai shiri da wani kamfanin haƙar ma'adanai ke yi domin bai wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kunya
- Gwamnati ta ce ba ta da wata alaƙa ta doka ko ta kwangila da kamfanin ma’adinai mai suna Jupiter Lithium da ke wannan shirin
- Ana ganin shirin ba zai rasa nasaba da yadda hukumomin Najeriya suka soke wasu lasisin haƙar ma’adinai ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ma’aikatar Ma’adinai ta Tarayya ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta gano wata makarkashiya da ake shirya wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ma'aikatar ta danganta shirin da wani kamfani mai suna Jupiter Lithium, inda ta tabbatar da cewa babu wata alaƙa tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa Mai magana da yawun ma’aikatar, Segun Tomori, ya ce an ja hankalin gwamnati kan shirin Jupiter na ƙaddamar da yaɗa labaran ƙarya kan Najeriya.
Ana shirya wa Tinubu gadar zare a UK
TVC News ta wallafa cewa Segun Tomori, ya bayyana cewa ana shirya yaɗa karairayi a kan Najeriya a lokacin ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai Birtaniya.
A cewarsa, a farkon makon nan mai ba ministan ma’adinai shawara na musamman kan hulɗa da jama’a, Kehinde Bamigbetan, ya rubuta martani kan wani rahoto.
A rahoton an yi zargin kamfanin Jupiter ya ɗauki nauyin wallafawa mai taken cewa Najeriya ta kwace wani aikin lithium na Birtaniya da sojoji.
Martanin gwamnatin ya ce:
“A fannin ma’adinai na Najeriya, doka ba ta fifita kowa ba."
Gwamnati ta fallasa yadda wasu mutane, daga ciki har da Steve Davis da Hamish MacDonald, suka yi amfani da hanyoyi na yaudara wajen gudanar da harkokin ma’adinai.

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya faɗi dalilin da ya sa ƴan ta'adda suka fi kai hare hare a Ramadan
Tomori ya jaddada cewa zarge-zargen da ake yadawa ba su da tushe balle makama, yana mai cewa babu wata hulɗa tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Jupiter Lithium.
Gwamnatin Tinubu ta kawo canji haƙar ma'adanai
Ma’aikatar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga soke wasu lasisin haƙar ma’adinai na kamfanin Basin Mining, wani kamfani na Najeriya da ake dangantawa da wani ɗan Australiya mai suna Steve Davis.
A cewar gwamnati, an soke lasisin ne bayan kamfanin ya gaza biyan wasu wajibai na kuɗi da dokokin ma’adinai suka tanada.
Tomori ya ce kamfanin ya kasa biyan kudin hidimar shekara da suka kai Naira biliyan 2.494 na shekarun kasafin kuɗi na 2024 da 2025.

Source: Facebook
Lasisi da abin ya shafa sun haɗa da 45454ML, 45117ML, 45118ML, 40532ML da 40533ML, waɗanda aka soke bayan an aika wa kamfanin sanarwa bisa ga dokokin da ake bi.
Haka kuma, ma’aikatar ta karyata zargin cewa an miƙa lasisin ga wani kamfanin kasar Sin, tana mai cewa wannan ƙage ne da aka kirkira domin ruɗar da jama’a da al’ummar duniya.

Kara karanta wannan
Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran
Gwamnati ta kuma ce Davis yana da alaƙa da wasu kamfanonin ma’adinai da dama a Najeriya, daga ciki har da Comet Minerals Ltd, Range Mining Ltd, Northern Numero Ltd, Sunrise Minerals Ltd da Iron Ore Mining Ltd.
Yadda Tinubu ya yi amfani da barazanar Trump
A baya, mun wallafa cewa farkon watan Nuwambar 2025, wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a kafafen sada zumunta ya jawo damuwa a Najeriya.
Donald Trump wanda ya sake lashe zabe a 2024 ya yi ikirarin cewa Amurka na shirin shiga Najeriya da makamai saboda abin da ya kira kashe Kiristoci a kasar.
Sai dai Shugaba Tinubu ya ƙaryata hakan, inda ya yi amfani da wannan dama wajen barin sojojin Amurka su shigo ƙasar domin a taimaka wajen yaƙar ta'addanci.
Asali: Legit.ng
