Siyasar Kano Ta Dau Zafi: Abba Ya Cire Mataimakin Gwamna daga Mukamin Kwamishina
- Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya rushe ma’aikatar ilimi mai zurfi tare da cire Kwamishinansa da ke jagorantarta
- Mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo shi ne kwamishina a ma'aikatar wanda ya rasa kujerarsa saboda rikicin siyasa
- Matakin ya zo ne bayan rahotannin cewa majalisar dokokin Kano ta tura wa mataimakin gwamnan takardar fara tsige shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rushe ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ke jagoranta.
Matakin ya tilasta wa mataimakinsa, Gwarzo rasa mukaminsa na kwamishinan ma’aikatar.

Source: Facebook
Abba ya cire mataimakinsa a muƙamin kwamishina
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature ya wallafa a Facebook ta bayyana cewa matakin na daga cikin sababbi gyare-gyare da gwamnati ke yi a bangaren ilimi.
A cewar sanarwar, sake fasalin ma’aikatun zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin sassa, kawar da maimaita ayyuka, da kuma rage yawan kashe kuɗin gwamnati.
Wannan ci gaban ya biyo bayan tashin hankalin siyasa da ya biyo bayan rahoton cewa majalisar dokokin Kano ta miƙa wa mataimakin gwamnan takardar fara tsige shi.
Rahotanni sun nuna cewa yunƙurin tsige mataimakin gwamnan yana da alaƙa da sabanin siyasa, bayan da ake zargin Gwarzo ya ƙi bin gwamna Yusuf zuwa jam’iyyar APC.
A sabon tsarin da aka ƙaddamar, ma’aikatar ilimi mai zurfi za a haɗa ta da ma’aikatar ilimi, wadda yanzu za ta kula da dukkan harkokin ilimi a Kano.

Source: Original
Sauye-sauye da za a yi a ma'aikatar
Haka kuma za a kafa wata sabuwar darakta mai kula da ilimi mai zurfi a cikin ma’aikatar, wadda za ta rika tafiyar da harkokin jami’o’i da sauran makarantu.
Wannan darakta za ta kasance ƙarƙashin jagorancin babban sakatare na dindindin tare da ma’aikata domin tabbatar da ingantaccen tafiyar da harkokin ilimi mai zurfi.
Sanarwar ta ce hukumomi da ke ƙarƙashin tsohuwar ma’aikatar, ciki har da hukumar bayar da tallafin karatu, za su koma ƙarƙashin ma’aikatar ilimi.
Haka kuma jami’o’in da gwamnatin Kano ta mallaka da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi za su kasance ƙarƙashin kulawar sabuwar daraktar a cikin ma’aikatar ilimi.
Gwamna Abba ya ce matakin sake fasalin ya nufi ƙara inganci, ƙarfafa gaskiya a aiki, da kuma inganta yadda ake tafiyar da harkokin ilimi a Kano.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sababbi gyare-gyare domin farfaɗo da bangaren ilimi da kuma ƙara wa matasa damar samun ilimi.
Gwamnan ya kuma umarci ofishin sakataren gwamnatin Kano da ofishin shugaban ma’aikata su tabbatar an aiwatar da sauye-sauyen ma’aikatun cikin gaggawa da sauƙi.
Abba Kabir ya gargadi kwamishinoninaa a Kano
A wani labarin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi 'yan majalisar zartarwa su daina fitar da bayanan gwamnati sakaka ga jama'a.
Ya ce dole su hada kai domin ci gaban Kano da jin dadin al’umma, kuma ba za a kara lamuntar masu kawo tasgaro ga haka ba.
Gwamnan ya kuma tabbatar da murabus na kwamishinoni biyar bayan gwamnatin jihar ta sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
Asali: Legit.ng

