Malamin Musulunci na Zargin an Ware N500bn ga Malamai, Sarakuna kan Zaben 2027
- Wani malamin Musulunci a Najeriya ya ce an ware kimanin N500bn domin shirye-shiryen samun nasara a zaben 2027
- Malamin ya ce an shirya kafa kwamiti na malaman addini da sarakunan gargajiya, inda ya ce wani fasto ne zai jagoranta
- Shehin ya bayyana cewa an nemi ya shiga cikin shirin amma ya ce ba shi da hannu a ciki inda ya yi watsi da su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wani malamin Musulunci, Sheikh Sanusi Khalil a Najeriya ya yi magana kan shirin da yan siyasa ke yi game da zaben shekarar 2027.
Malamin ya ce an ware biliyoyin kudi wanda za a yi amfani da su domin samun nasara a zaben 2027 da ke tafe.

Source: Facebook
Shehin malamin ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta gano a shafin @UI_Wakilii da ya wallafa a shafin X.
2027: Malami ya yi zargin ware makudan kudi
A cikin bidiyon, malamin ya ce an ware N500bn domin hada kwamitin malaman addini da sarakunan gargajiya.
Ya ce an shirya abin wanda wan Fasto ne ke jagorantar kwamitin domin ci gaba da neman mutane kan zaben 2027.
Ya ce:
"Akwai kudi N500bn, miliyan sau dubu sau 500, wannan kudin ake son a samu kwamiti na malaman addini da sarakunan gargajiya.
"Ana son wanda zai jagoranta kuma yana da kashi biyar na wannan N500bn, aka ce min malam ko da ya ke mun san baka son wannan abu amma abu ne idan aka kyale menene, menene.
"Na ce to ka san dai ba ruwana da shi ko, sai ya ce to kuma daman akwai wani Fasto shi ke jagorantar abin, na ce to ai ka riga ka gama yanke hukunci bana yi."

Source: Facebook
Malam ya zargi masu tallan Muslim/Muslim
Malamin ya ce wannan fa bangaren Musulmi ne tukuna, ba a yi maganar bangaren Kiristoci ba.
Dalilin haka, malamin ya ce duk wanda ka ga yana Muslim/Muslim to watakila an kawo masa ziyara ne da labarin kudin da aka ware.
"Ya ce a'a malam bari in kira maka Fasto din, na ce uwaka da Fasto din, na ce ku je ku yi ta yi ba ruwa na kai da Allah.
"Wannan fa bangaren Musulmi ne fa, to bangaren Kiristoci fa, saboda haka ni ina magana ne a kan dalili, idan ka ga malami yana tsare ido yana Muslim/Muslim anya ba su kai masa labari ba kuwa."
- Sheikh Sanusi Khalil
Farfesa Maqari ya magantu kan juyin mulki
A wani labarin, limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya yi magana game da tsare mutanen da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki.
Malamin ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce da yawa daga cikin manyan jami'an gwamnati suna tsoron tunkararsa da batun.
Babban malamin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Sani Khalifa Zariya na cikin wadanda aka kama aka tsare kusan sama da wata uku da suka wuce.
Asali: Legit.ng

