Tarihi: Musulmi Za Su Samu Hutun Ranakun Salla a Amurka bayan Kudirin Ɗan Majalisa

Tarihi: Musulmi Za Su Samu Hutun Ranakun Salla a Amurka bayan Kudirin Ɗan Majalisa

  • Ɗan majalisar California, Matt Haney, ya gabatar da kudirin doka AB 2017 domin ba Musulmi damar gudanar da bukukuwan salla
  • Kudurin ya ba makarantun gwamnati da kwalejojin al'umma damar rufe makarantu a ranakun Sallah tare da bai wa ɗalibai damar yin hutu daga zuwa makaranta
  • Idan dokar ta wuce, California za ta zama jiha ta biyu a Amurka bayan Washington da ta amince da hutun hukuma domin bukukuwan Musulunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

California, US - Ɗan majalisar jihar California, Matt Haney, ya sanar da wani sabon kudirin doka mai lamba AB 2017 a ranar 12 ga Maris, 2026.

Kudurin na neman ayyana ranakun Babbar Sallah da Karamar Sallah a matsayin hutun hukuma a jihar wanda zai faranta wa Musulmi rai.

Dan majalisa ya kawo kudiri domin samar wa Musulmi damar hutu a salla
Dan majalsa daga California bayan gabatar da kudiri a majalisa. Hoto: @matthaneysf.
Source: Instagram

Amurka: Ana shirin kawo kudirin da zai taimaki Musulmi

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da za su hana Donald Trump iya cewa ya yi nasara kan Iran

An fara gabatar da kudurin ne tun ranar 17 ga Fabrairun 2026 tare da goyon bayan wasu mambobin majalisa, cewar rahoton TRT Hausa.

Dokar na da nufin bai wa makarantu da kwalejojin gwamnati damar dakatar da karatu a ranakun Sallah domin samun natsuwa a wadannan lokuta.

Har ila yau, kudurin zai sanya ranakun Sallah cikin jerin kwanakin da ɗalibai za su iya amfani da su domin yin hutu daga zuwa makaranta ba tare da wata matsala ba.

A karkashin dokar, ma’aikatan gwamnatin jihar za su iya amfani da hutunsu na shekara ko wasu ranakun hutu domin gudanar da ibada a lokacin bukukuwan Sallah.

Sai dai an bayyana cewa dokar ba za ta shafi ma’aikatan bangaren shari’a ba, domin ba za a ɗauki ranakun Sallah a matsayin hutun aiki a gare su ba.

Manufar kudurin ita ce kawo ƙarshen rashin ware ranakun bukukuwan Musulunci biyu mafi muhimmanci a hukumance a jihar California, kamar yadda ake yi wa Kirsimeti.

Dan majalisa na neman a ba Musulmi damar hutun salla a Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Carlifornia za ta kafa tarihi bayan Washington

Idan majalisar ta amince da dokar, California za ta zama jiha ta biyu a Amurka bayan Washington da ta riga ta ayyana ranakun Sallah a matsayin hutun hukuma.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Wani babban jirgin dakon man Amurka ya rikito daga sararin samaniya

Al'ummar Musulmi na kara yawa a Amurka wanda hakan ke kara yawan bukukuwan sallah da ake yi a fadin kasar.

Birnin New York shi ne garin da Musulmi suka fi yawa da aka ce sun kai akalla fiye da 700,000 sai kuma mai bi masa shi ne birnin Carlifornia da yawan su ya kai 504,000, cewar Indian Eagle.

Mamdani ya yi rantsuwa da Alkur'ani

A baya, mun ba ku labarin cewa zababben magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya kafa tarihi ta hanyar amfani da Alƙur’ani wajen rantsar da shi bayan lashe zabe.

Matashin ɗan siyasar zai zama Musulmi na farko da kuma ɗan Afirka na farko da aka taɓa zaɓa a wannan muƙami mai muhimmanci.

Rahotanni sun bayyana cewa zai sha rantsuwar ne da wani Alƙur’ani mai ɗauke da tarihin al’ummar Musulmi da baƙar fata a birnin New York da ke Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.