Lauya Ya Kitsa Wa Gwamnatin Tinubu Yadda Za Ta Tursasa Wa Trump Kawo Karshen Yaki da Iran

Lauya Ya Kitsa Wa Gwamnatin Tinubu Yadda Za Ta Tursasa Wa Trump Kawo Karshen Yaki da Iran

  • Babban lauya a Najeriya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya yi magana kan yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Femi Falana ya bayyana cewa akwai rawar da Najeriya za ta iya takawa domin ganin an kawo karshen rikicin da ake yi
  • Babban lauyan ya bayyana cewa za a iya matsawa Shugaba Donald Trump lamba domin kawo karshen zubar da jinin da ake yi

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana, ya ba Najeriya shawara kan yakin da ake yi tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran.

Femi Falana ya buƙaci Najeriya da ta haɗa kai da sauran ƙasashe domin matsa wa Amurka lamba ta diflomasiyya game da ayyukanta a cikin rikicin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Amurka ta je barbara, za ta iya dawo wa da ciki a yakin Iran

Femi Falana ya ba gwamnatin Tinubu shawara
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump
Source: Facebook

Babban lauyan ya yi wannan kiran ne yayin wata hira a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.

Wace shawara aka ba Gwamnatin Tinubu?

A cewarsa, dole ne gwamnatin Najeriya ta yi aiki da sauran ƙasashe don tabbatar da bin dokokin ƙasa da ƙasa, sannan ta ƙarfafa manyan ƙasashe irin su Rasha da China su shiga tsakani a wannan rikici da ke ƙara ta’azzara.

Ya soki ayyukan Donald Trump, inda ya zargi shugaban na Amurka da yin watsi da dokokin ƙasa da ƙasa da ƙudurin majalisar dinkin duniya.

“Shugaba Trump yana nuna raini ga dokokin ƙasa da ƙasa. Don haka, ya janye Amurka daga kusan ƙuduri 66 na Majalisar Ɗinkin Duniya. A gare shi, kudurin majalisar dinkin duniya ba su da wani amfani."

- Femi Falana

Ana son Najeriya ta hada kai da kasashe

Babban lauyan ya lura cewa ya kamata Najeriya ta farfaɗo da al’adarta ta diflomasiyya ta bangarori da dama, ta hanyar yin aiki da sauran ƙasashe don neman sulhu.

Kara karanta wannan

"Sai an cika su"; Iran ta kafa sharuddan kawo karshen yaki da Amurka, Isra'ila

“Aikinmu a matsayinmu na ƙasa, kamar yadda muka saba yi a baya, shi ne mu haɗa kai da sauran ƙasashe. Dole ne mu matsa da sauri yanzu don haɗa kai da sauran ƙasashe domin matsa wa Trump lamba."

- Femi Falana

Falana ya ba gwamnatin Tinubu shawara
Babban lauya a Najeriya, Femi Falana Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Falana ya fadi kasashen da za a lallasa

Falana ya kuma jaddada muhimmancin shawo kan manyan ƙasashen duniya irin su Rasha da China don su shiga tsakani ta hanyar diflomasiyya, yana mai cewa suna da tasiri sosai a kan Iran.

“Muna bukatar mu lallashi China da Rasha su shiga tsakani domin su ne ƙasashe biyu da Iran za ta saurara,”

- Femi Falana

Bayan ɓangaren rikicin na duniya, Falana ya yi kiran da Najeriya ta ƙarfafa tsarinta na tsaro na gida tare da rage dogaro ga ƙasashen waje don tabbatar da zaman lafiya.

Iran za ta farmaki sababbin wurare a Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamanda a rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran, Janar Majid Mousavi, ya ce za su farmaki sababbin wurare a Isra'ila.

Janar Mousavi ya bayyana cewa wuraren hako iskar gas na Isra'ila da ke Leviathan da Karish, waɗanda ke cikin tekun Mediterranean, sun zama wuraren da za a kai wa hari.

Kwamandan na IRGC ya nuna cewa ba a iya wadannan wuraren za su tsaya ba, akwai wasu wurare da dama da za su farmaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng