Bayan Harin Boko Haram da Ya Girgiza Sojoji, Tinubu Ya Canza Taku game da Tsaro

Bayan Harin Boko Haram da Ya Girgiza Sojoji, Tinubu Ya Canza Taku game da Tsaro

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen sababbin kayan aikin soja domin karfafa yaki da ta’addanci a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan shugabannin rundunonin soji sun gabatar wa shugaban kasa cikakken rahoto kan halin tsaro
  • Gwamnati ta ce sababbin matakan da aka dauka za su taimaka wajen karfafa rundunonin tsaro su doke ‘yan ta’adda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin sayo karin kayan aikin soja domin karfafa yakin da rundunonin tsaro ke yi da kungiyoyin ta’addanci a fadin Najeriya.

Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan bayan ya jagoranci shugabannin rundunonin tsaro zuwa Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Nuru Khalid da malaman da aka dakatar daga wa'azi kafin Alkali Zariya

Tinubu ya sahale a karo kayan aikin yaki da rashin tsaro
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a wajen wani taro Hoto: Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Janar Christopher Musa ya ce shugabannin sojojin sun gabatar wa shugaban kasa cikakken bayani kan yadda ayyukan tsaro ke gudana a sassan kasar nan.

Shugabannin sojoji sun gana da Bola Tinubu

Trust radio ta ruwaito cewa a cewarsa, taron ya bai wa shugaban kasa damar samun cikakken bayani kai tsaye daga wadanda ke jagorantar ayyukan soji a kasa.

Ya ce wasu rahotannin kafafen yada labarai kan hare-haren ‘yan ta’adda ba su nuna cikakken yadda sojoji ke gudanar da ayyukansu ba.

Ministan tsaron ya amince cewa an samu wasu hare-hare a wasu yankuna na kasar nan a baya-bayan nan, amma ya jaddada cewa rundunonin tsaro suna mayar da martani yadda ya kamata.

'Sojoji na samun nasara' - Christopher Musa

Ministan ya ce sojoji sun ci gaba da tunkarar ‘yan ta’adda tare da yi masu mummunar illa a lokuta da dama a yakin da ake yi da miyagun da sauran masu tayar da kayar baya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya juyo Arewa, ya zabo mutumin da yake so ya zama mataimakin gwamnan CBN

Shugabannin tsaro sun ana da Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da shugabannin rundunonin tsaro Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa a sababbin farmakin da aka kai, an kashe wasu manyan shugabannin ‘yan ta’adda tare da kwace kayayyakin su na yaki.

A cewarsa, wannan na nuna cewa rundunonin tsaro na ci gaba da samun nasarori duk da kalubalen da ake fuskanta na asarar rayuka da sauransu matsaloli a yayin aiki.

Ministan ya kuma yi alhinin rasuwar wasu jami’an tsaro da suka mutu yayin gudanar da ayyukansu, yana mai cewa mutuwarsu abu ne mai matukar tayar da hankali.

Ya bayar da tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya za ta ci gaba da aiki tukuru wajen kare rayuka da dukiyoyin talakawan kasar nan.

Shugaba Tinubu ya kara albashin sojoji

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin albashi ga dakarun sojojin Najeriya da kuma alawus na musamman ga jami'an dake gadin Aso Rock.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan an samu rahoton cewa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28,000 don karfafa tsaro a fadin Najeriya domin inganta tsaro.

Kara karanta wannan

Taɓarɓarewar tsaro: Minista ya shiga ganawar gaggawa da shugabannin sojoji

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta tura jirage masu saukar ungulu zuwa Benuwai domin taimakawa a wajen fatattakar 'yan ta'adda da suka addabi jama'a a sassan jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng