Kotu Ta Jika Wa El Rufai Aiki, Ta Amince da Bukatar Hukumar ICPC
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja na ci gaba da sauraron shari'ar da ake yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da hukumar ICPC
- A zaman kotun na ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026, ta amince da wata bukata da hukumar ICPC ta gabatar
- Alkalin kotun ta bayyana cewa ta amince da bukatar ne domin ba hukumar ICPC damar gudanar da bincike
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar yaki da rashawa ta ICPC a shari'ar ta da Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Kotun ta ba hukumar ICPC izinin bincika tare da nazarin na'urorin da aka kwashe daga gidan tsohon gwamnan na jihar Kaduna.q

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce alkalin kotun, mai shari'a, Joyce Abdulmalik, ta bayar da wannan umarnin a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.
Mai shari'a Joyce Abdulmalik wadda ke jagorantar shari'ar ta ba da umarnin ne biyo bayan wata buƙata ta gaggawa da hukumar ICPC ta shigar.
Bukatar ICPC ta samu shiga a kotu
Yayin gabatar da buƙatar, lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya buƙaci kotun da ta ba hukumar damar samun damar yin amfani da na'urorin don dubawa da kuma gudanar da bincike na kimiya, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Akponimisingha ya shaida wa kotun cewa wannan buƙatar ta zama dole domin ba wa masu bincike damar gudanar da nazarin kimiya da kwashe bayanai a matsayin wani ɓangare na binciken da ake gudanarwa wanda ya shafi tsohon gwamnan.
Mai shari'a, Joyce Abdulmalik ta tabbatar da cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa tana da haƙƙin bincikar abubuwan da aka kwace yayin gudanar da bincike don manufar nazarin kimiya.
El-Rufai na kalubalantar ICPC
Nasir El-Rufai ya ƙalubalanci binciken da hukumar ICPC ta gudanar a gidansa da ke Abuja a ranar 19 ga Fabrairu.
Tsohon gwamnan yana roƙon kotun da ta soke takardar izinin bincike da wata kotun majistare ta bayar a babban birnin tarayya Abuja a ranar 4 ga Fabrairun 2026, wadda ta ba da ikon bincike da kuma ƙwace kayayyaki a gidansa.

Kara karanta wannan
ICPC ta samu damar kara garkame El Rufa'i na kwanaki 14, akwai yiwuwar ya yi sallah a tsare
Haka kuma ya buƙaci kotun da ta hana waɗanda ake ƙara amfani da su ko gabatar da duk wani abu da aka ƙwace lokacin binciken a matsayin shaida a kowane irin bincike ko shari'a da ta shafe shi.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya kuma nemi umarnin kotu da ya tursasa wa ICPC da 'yan sanda su mayar masa da dukkan kayayyakin da aka ƙwace daga gidansa nan take, tare da cikakken jerin sunayen kayayyakin.
Sannan yana neman diyya ta N1bn kan asarar da aka jawo masa, da kuma horo ga hukumomin kan zargin tauye masa haƙƙoƙinsa na ɗan adam.
ICPC ta samu damar ci gaba da tsare El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar ICPC ta samu umarni daga kotu wanda ya ba ta damar ci gaba da tsare Malam Nasir El-Rufai.
A umarnin da hukumar ta samu, ta na da damar ci gaba da rike tsohon gwamnan na jihar Kaduna har na tsawon ƙarin kwanaki 14 a ofishinta.
Kotun ta ba da umarnin ne domin bai wa hukumar damar kammala binciken da take yi kan zarge-zargen da ake yi masa.
Asali: Legit.ng
