Dr Bashir Aliyu Ya Yi Kaca Kaca da Netanyahu kan Kama Masu Sukar Isra'ila a Arewa

Dr Bashir Aliyu Ya Yi Kaca Kaca da Netanyahu kan Kama Masu Sukar Isra'ila a Arewa

  • Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr Bashir Aliyu Umar ya caccaki hukumomin Najeriya bisa zargin kama masu sukar Benjamin Netanyahu
  • Sheikh Bashir Aliyu Umar ya bayyana cewa ana so a soke dokar zagin Annabi SAW amma kuma ana kama masu zagin Firaministan kasar Isra'ila
  • Kungiyar Amnesty International mai kare hakkin dan Adam ta yi zargin cewa hukumar DSS ta kama wasu mutane kan magana a kan yakin Iran da Amurka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - An fara korafi game da zargin kama masu sukar gwamnatin Isra'ila da Amurka kan kaddamar da hare-hare da suka yi a Iran, lamarin da ya jawo yaki a Gabas ta Tsakiya.

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr Bashir Aliyu Umar ya yi magana da babbar murya yana cewa ana son hana al'umma fadin albarkacin baki.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran

Dr Bashir Aliyu Umar yayin wa'azi a Kano
Dr Bashir Aliyu Umar yana wani wa'azi a Kano. Hoto: Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya nuna cewa kasar Isra'ila karkashin Benjamin Netanyahu ta aikata kisan kare dangi, inda ya yi tir da ita.

Bayanin Dr Bashir kan Netanyahu

Dr Bashir Aliyu Umar ya nuna damuwa kan yadda ya ce ana samun rahotanni da ke nuna ana kama mutane masu caccakar Isra'ila.

Malamin ya ce:

"Wadanda suka fadi ra'ayinsu kan kisan kare dangi da Isra'ila ta ke an kama su."

Malamin ya bayyana cewa ana kama mutane ne a daidai lokacin da aka ce dole a soke dokar da ta ce hukunta wanda ya zagi Annabi SAW amma ana kama masu zagin Benjamin Netanyahu.

Ya kara da cewa an daure wanda ya zagi Netanyahu amma wanda ya zagi Annabi SAW an ce yana da yancin fadin ra'ayinsa.

Sheikh Bashir ya ce:

"Mun fada Isra'ila kisan kare dangi ta ke, mun fada Netanyahu ya turo a kama mu."

Kara karanta wannan

Nuru Khalid da malaman da aka dakatar daga wa'azi kafin Alkali Zariya

"Da me za mu ji, rashin tsaro... sannan a ce ba za mu iya fadan ra'ayinmu ba. Wannan wane irin rashin 'yanci ne. Me ake so a mayar da mu?"

Gargadin Amnesty kan sukar Isra'ila

Kungiyar Amnesty International ta nuna matukar damuwa kan yadda hukumar DSS ke kara tsananta matakan murkushe ra’ayoyin da ake wallafawa a kafafen sada zumunta dangane da yakin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.

A sakon da ta wallafa a Facebook, Amnesty ta ce akalla mutane biyu aka tsare, kuma daya daga cikinsu na dab da fuskantar shari’ar da ake ganin ba ta da inganci bisa zarge-zargen da ake kallon su a matsayin marasa tushe.

Ta ce:

"Haka kuma mun samu rahotanni cewa ana gayyatar wasu masu sukar Amurka da Isra’ila zuwa ofishin DSS domin amsa tambayoyi."
Sani Waspapping da aka kama a Najeriya
Sani Waspapping da aka ce DSS ta kama a Kaduna. Hoto: Amnesty International
Source: Facebook

Kungiyar Amnesty ta ce daukar sukar manufofin gwamnatocin Amurka da Isra’ila a matsayin tayar da fitina karkatar da gaskiya ne.

Ga bidiyon bayanin Dr Bashir Aliyu Umar:

Yakin Iran: Netanyahu ya yi korafi

A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya fara korafi game da yakin da ya hada kai da Amurka suka kai Iran.

Kara karanta wannan

Ana tunanin azumi 30, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa ga musulman Najeriya

A wani bayani da ya yi, Netanyahu ya nuna cewa yakin zai jawo kashe makudan kudi wanda zai bukaci sauya fasalin kasafin kudin Isra'ila.

Duk da haka ya bayyana cewa yakin da suka shiga da Iran ya zama musu dole, kuma za su cigaba da hada kai da sojojin Isra'ila wajen kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng