Bayan Karyata Mutuwarsa, Netanyahu Ya Tura Kalubale ga Mojtaba Khamenei
- Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ba zai iya fitowa bainar jama’a ba
- Netanyahu ya ce Amurka da Isra'ila na “murkushe” gwamnatin Iran da kungiyar Hezbollah
- Mojtaba Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da kai hari kan sansanonin sojojin Amurka a yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kalubalanci sabon jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei.
Netanyahu ya ce sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, “ba zai iya nuna fuskarsa a bainar jama’a ba”.

Source: Getty Images
Netanyahu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 12 ga watan Maris din shekarar 2026 yayin wani taron manema labarai na farko tun bayan da Israel da Amurka suka fara kai hare-hare kan Iran, cewar France 24.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran
Netanyahu ya caccaki Ayatollah Mojtaba Khamenei
Netanyahu ya caccaki Khamenei yana mai kiran sa yar tsana na rundunar 'Islamic Revolutionary Guard Corps' ta kasar Iran.
A wajen taron, ya kuma ce Isra'ila da Amurka na “murkushe” gwamnatin Iran da kuma kungiyar Hezbollah da ke zaune a Lebanon.
Netanyahu ya kuma yi kira ga mutanen Iran, yana cewa lokaci na gabatowa da za su fara sabon tafarkin ‘yanci.
Ya ce kasashen Isra'ila da Amurka na tare da mutanen Iran, amma a karshe makomarsu tana hannunsu, cewar The Hindu.

Source: Getty Images
Netanyahu ya fadi alakarsa ta Donald Trump
Firaministan ya kuma bayyana shugaban Amurka, Donald Trump, a matsayin abokinsa na kusa wanda suke shawarwari game da shugabanci da sauran lamura.
Ya kara da cewa shi da Trump na yin magana kusan kullum, kuma suna yanke muhimman shawara kan yakin tare.
A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa Mojtaba Khamenei bai fito bainar jama’a ba tun bayan da ya gaji mahaifinsa a matsayin babban jagoran Iran.
Jawabin farko da Mojtaba Khamenei ya yi
Sai dai a yau Alhamis, ya gabatar da jawabinsa na farko tun bayan hawansa kan mulki, wanda aka watsa a gidan talabijin na gwamnatin Iran.
Jawabin dai mai gabatarwa ne ya karanta shi a talabijin, ba tare da Khamenei ya bayyana da kansa ba.
A cikin jawabin, ya ce gwamnatin Iran ta yi nasarar dakile yunkurin da ake yi na tayar da zaune tsaye a kasar.
Ya kuma jaddada cewa Iran dole ta ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke kasashen makwabta.
Haka kuma ya yi kira da a rufe dukkan sansanonin sojojin Amurka da ke yankin tare da ci gaba da amfani da matakin rufe mashigar Hormuz domin matsin lamba.
Mojtaba Khamenei ya yi jawabin farko a Iran
A wani labarin, an ji cewa sabon jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei ya yana wa jami'an tsaron kasar yayin da akeci gaba da yaki.

Kara karanta wannan
Bayan kwana 10 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila ya mika bukata 1 ga mutanen Iran
Mojtaba Khamenei ya bayyana haka ne yayin jawabin farko tun bayan nada shi jagoran addinin Musulunci a Iran.
Nadin Mojtaba Khamenei na zuwa ne bayan kisan mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.
Asali: Legit.ng
