Yaƙin Iran/Isra'ila: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Ƙayyade Farashin Fetur

Yaƙin Iran/Isra'ila: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Ƙayyade Farashin Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan farashin man fetur a Najeriya yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya tun karshen Fubrairu
  • Ta ce ba za ta saka hannu wajen kayyade farashin fetur ba duk da tashin hankali a yankin da ya jawo sauye-sauyen farashin mai
  • Ministan kudi Wale Edun ya ce gwamnati za ta bullo da wasu matakai domin rage nauyin tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta game da kayyade farashin man fetur a Najeriya a sakamakon tashin da yake yi a yau.

Gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta tsoma baki wajen kayyade farashin fetur ba duk da rikicin da ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan farashin fetur a kasuwannin duniya
Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Federal Ministry of Finance.
Source: Facebook

Ministan kudi, Wale Edun, shi ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels a Abuja.

Kara karanta wannan

An gano mafitar illar da rikicin Iran da Isra'ila ke neman yi wa tattalin Najeriya

Iran/Isra'ila: Kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi

Edun ya ce gwamnati na duba wasu hanyoyi domin rage tasirin rikicin da ya hada Amurka, Isra’ila da Iran.

Ministan ya ce tuni Bola Ahmed Tinubu ya sanar da samar da karin kayan sauya motoci 100,000 zuwa amfani da iskar gas ta CNG.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da daukar irin wadannan matakai maimakon tsoma baki cikin tsarin farashin kasuwa.

A cewarsa, gwamnati kan shiga ne kawai idan kasuwa ta gaza aiki yadda ya kamata amma ba a yanzu da ba a san makomar yakin ba

Gangar man fetur ta yi tsada a duniya

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tashin farashin danyen mai a duniya, a ranar 9 ga Maris, 2026 farashin ganga ya haura $100, mafi girma tun watan Yuli na shekarar 2022.

Washegari farashin ya ragu zuwa $87, ma’aikatar kudi ta ce rikicin na iya shafar farashin danyen mai na Najeriya, kudaden jarin kasuwanni da kuma kudin jigilar kayayyaki a duniya.

Kara karanta wannan

Ganin fetur ya tashi a duniya, Tinubu ya bada umarnin gaggawa a kawo wa 'yan Najeriya sa'ida

Sakamakon tashin farashin danyen mai da farashin fetur daga matatun mai, farashin da gidajen mai ke sayarwa ya karu sosai, hakan ya sa kudin sufuri ya ninka a wasu manyan hanyoyi a Najeriya.

Minista ya yi magana kan kayyade farashin fetur a Najeriya
Babban ministan kudi a Najeriya, Wale Edun. Hoto: Federal Ministry of Finance.
Source: Twitter

Yadda yakin Iran/Isra'ila ke shafar Najeriya

Edun ya ce sauye-sauyen farashin fetur daga kamfanoni masu zaman kansu, musamman matatar Dangote, na nuna yadda kasuwa ke tafiya a halin yanzu.

Ya ce matatar ta rage farashin fetur daga kusan N1,200 zuwa sama da N1,000, a cewarsa, wannan yana nuna yadda farashin kasuwa ke hawa da sauka.

Ministan ya ce Najeriya na da damar tace danyen mai zuwa sinadarai da kayayyakin mai.

Edun wanda yake ofis tun a watan Agustan 2023 ya kara da cewa wasu kasashe kamar Amurka na kokarin bude sababbin matatun mai yanzu.

Edun ya kuma yabawa jarin kamfanoni masu zaman kansu a fannin tace mai, musamman wanda Aliko Dangote ya jagoranta.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan yakin Iran/Isra'ila

An ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce za ta iya gyara manufofin tattalin arziki idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya tsananta.

Ta ce za ta dauki matakan ne domin kare tattalin arzikin Najeriya duba da yadda rikicin ke neman dagula wasu ɓangarori.

Gwamnati ta ce hauhawar farashain makamashi, janyewar jari da matsalar hanyoyin sufuri na duniya na iya shafar farashi da tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.