Rokon da Rasha Ta Yi ga Iran da Isra'ila yayin da Yaƙi Ke Kara Kamari a tsakaninsu
- Kasar Rasha ta tura sakonni na musamman ga Iran da Isra'ila game da ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Rasha ta bukaci Amurka da Isra’ila su dakatar da hare-haren da suke kai wa Iran, tare da komawa kan tattaunawa
- Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta ce Moscow na kokarin samar da matakan da za su rage rikicin ta hanyar diflomasiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Moscow, Russia - Kasar Rasha ta kuma tsoma baki game da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka wacce ke bugan kirji kan nasarar da suke samu.
Kasar Rasha ta bukaci Amurka da Isra’ila su dakatar da hare-haren da suke kai wa Iran, tare da komawa kan teburin tattaunawa domin rage tashin hankali.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100

Source: Getty Images
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta bayyana cewa Moscow na matsa lamba domin daukar matakan da za su rage rikici, cewar Al Jazeera.
Abin da Putin ya tattauna da Shugaban Iran
Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar Shugaba Vladimir Putin da kuma Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian kan yakin da ake yi.
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya kira waya inda suka tattauna da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian game da yakin da yaki karewa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Putin ya tattauna da Pezeshkian kan yakin Iran da Isra'ila mai goyon bayan kasar Amurka.
Fadar Kremlin ta ce yayin tattaunawar, Putin ya jaddada matsayinsa na goyon bayan dakatar da rikicin da wuri domin rage tashin hankali.

Source: Getty Images
Iran/Isra'ila: Dalilin Rasha na neman a tattauna
Rasha ta ce wadannan matakai na da nufin dawo da rikicin kan hanyar diflomasiyya, inda kasashe za su warware matsalolin ta hanyar tattaunawa.
Zakharova ta kuma yi gargadi cewa halin jin kai a yankin Gabas ta Tsakiya ya kara tabarbarewa sakamakon ci gaba da fadan, cewar Reuters.
Ta kara da cewa karuwar hare-hare da martani tsakanin bangarorin da ke rikici na matukar tayar da hankali ga kasashen duniya.
Kiran na Rasha ya zo ne yayin da kasar ke ci gaba da yakin da take yi da Ukraine, wanda yanzu ya shiga shekara ta biyar.
An kwashe kusan mako biyu kenan ana gwabza yaki tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka wanda ya jawo asarar rayukan dubban mutane.
Rasha ta musanta zargin taimaka wa Iran
An ji cewa majiyoyi sun bayyana cewa kasar Rasha ta yi martani game da zarginta da ake yi da ba da bayanan sirrin sojojin Amurka ga Iran a yakin da ake yi.
Maganar ta fito ne bayan tattaunawar waya tsakanin Shugaba Donald Trump da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya.
Rahoto ya zargi Moscow da bai wa Tehran bayanan wuraren jiragen ruwan yaki da jiragen sama na Sojojin Amurka a yankin wanda aka kai masu hare-hare.
Asali: Legit.ng
