Malamin Addini Ya Cire Tsoro, Ya Gayawa Shugaba Tinubu Halin da 'Yan Najeriya Ke Ciki
- Tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Samson Ayokunle, ya nuna rashin gamsuwa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Samson Ayokunle ya bayyana cewa 'yan Najeriya na ji a jikinsu sakamakon manufofin da Shugaban kasa ya bullo da su
- Faston kuma tsohon shugaban na kungiyar CAN, ya bukaci gwamnati ta sake salo domin tsamo 'yan Najeriya daga halin da suke ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Samson Ayokunle, ya soki manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Samson Ayokunle ya bayyana cewa ’yan Najeriya da dama suna ƙara talaucewa sakamakon yawaitar haraji da matsin tattalin arzikin da sababbin manufofin gwamnati suka haifar.

Source: Facebook
Tsohon shugaban na CAN ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a cikin shirin 'Inside Sources' na tashar Channels Tv, a ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026.
Me malamin ya ce kan manufofin Tinubu?
Ayokunle ya ce tasirin haraji mai yawa da kuma janye tallafin man fetur sun dagula yanayin kuɗi na 'yan ƙasa da dama.
A cewar malamin addinin Kiristancin, matsin lamba daga hauhawar farashin kayayyaki da kuma harajin da gwamnati ta sanya na barin ’yan Najeriya da dama suna shan wahala wajen biyan buƙatun yau da kullum.
“Mutane suna bayyana a matsayin matsiyata saboda abin da na ke gani a matsayin haraji marar ƙarewa. Ganin cewa, gwamnati ba ta damu da inda kuɗin suke fitowa ba."
- Samson Ayokunle
Ya ce 'yan Najeriya na shan wuya
Ya lura cewa ko ma tsofaffin ma’aikata da suka yi wa kasa hidima cikin aminci ba su tsira daga wannan matsi ba, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa ga ƙasar da ke fama da ƙalubalen tattalin arziki.
“Hatta mutanen da ba su aiki yanzu, mutanen da suka yi wa kasa hidima kuma suke amsar fansho, ana sanya musu haraji, ana tilasta musu su je su sayi man fetur domin zirga-zirga a kan farashi mai tsada."
- Samson Ayokunle
Gwamnatin Tinubu ta kawo sauye-sauye
Sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya a shekarun baya-bayan nan sun haɗa da janye tallafin man fetur da ƙoƙarin ƙara kudaden shiga na gwamnati ta hanyar faɗaɗa karɓar haraji.
Yayin da hukumomi ke cewa waɗannan matakan sun zama dole don daidaita tattalin arziki da kuma samar da kuɗaɗen ayyukan ci gaba, Ayokunle ya jayayya da cewa manufofin sun zo da sakamako mai tsanani ga talakawa.
Ya yarda cewa gwamnati ta ƙaddamar da sauye-sauyen ne da nufin inganta yanayin tattalin arzikin ƙasar, amma ya dage cewa ba a bayyana isassun matakan rage raɗaɗi ga ’yan ƙasa ba.

Source: Facebook
Wace shawara ya ba gwamnati?
Tsohon shugaban na CAN ya jaddada buƙatar hukumomin gwamnati na su fito da ingantattun hanyoyin kariya ga gajiyayyu don kare ’yan Najeriya masu rauni daga wannan yanayi mai tsauri.
Haka kuma ya yi kiran da a fito da sahihin bayani kan yadda alfanun sauye-sauyen tattalin arziki za su isa ga talakawa, inda ya yi gargaɗin cewa rashin magance halin ƙuncin da ake ciki na iya ƙara fushin al'umma.
Tinubu ya tausayawa 'yan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tausayawa 'yan Najeriya saboda tsadar man fetur.
Tinubu ya umarci a gaggauta rarraba kayan sauya injin mota zuwa mai amfani da iskar gas (CNG) kimanin 100,000 a duk fadin Najeriya.
Umarnin shugaban kasar wani bangare ne na kokarin gwamnati na rage kudin sufuri da kuma fadada amfani da makamashi na daban.
Asali: Legit.ng


