An Gano Mafitar Illar da Rikicin Iran da Isra’ila ke Neman Yi wa Tattalin Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta ce za ta iya gyara manufofin tattalin arziki idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya tsananta
- Ta ce za ta dauki matakan ne domin kare tattalin arzikin Najeriya duba da yadda rikicin ke neman dagula wasu ɓangarori
- Gwamnati ta ce hauhawar farashin makamashi, janyewar jari da matsalar hanyoyin sufuri na duniya na iya shafar farashi da tattalin arzikin Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi magana game da ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila a Gabas da Tsakiya.
Gwamnatin ta bayyana cewa tana shirye ta sake daidaita wasu manufofin tattalin arziki idan ya zama dole.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da Punch ta samu, gwamnati ta ce za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da daukar matakan manufofi idan ya zama dole domin rage matsaloli.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100
Yadda rikicin Iran/Isra'ila zai shafi Najeriya
Ta ce wannan rikici na iya jawo sababbin matsaloli ga tattalin arzikin Najeriya ta hanyar farashin makamashi, zuba jari da kuma harkar samar da kayayyaki a duniya.
Sanarwar da ma’aikatar kudi ta fitar ta ce Kwamitin Gudanar da Tattalin Arziki karkashin jagorancin ministan kudi, Wale Edun, ya fara nazarin yiwuwar tasirin rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.
Ma’aikatar ta ce an gudanar da taro kan shirin 'Naira-for-Crude' inda aka tattauna halin da kasuwar makamashi ta duniya ke ciki da kuma yadda hakan zai iya shafar tattalin arzikin Najeriya.

Source: Getty Images
Iran/Isra'ila: Hanyoyi 3 da yaki zai shafi Najeriya
Sanarwar ta ce rashin tabbas a duniya ya karu saboda fargabar katse hanyoyin samar da makamashi musamman mashigin Hormuz, wanda ke haddasa sauyin farashin danyen mai da kasuwannin kudi.
Jami’ai sun bayyana hanyoyi uku da rikicin zai iya shafar Najeriya, na farko shi ne sauyin farashin danyen mai da iskar gas wanda ke kara tsadar man fetur, dizal, gas na girki da kuma taki a cikin gida.
Na biyu shi ne kasuwannin kudi da zuba jari, inda karin rikicin siyasa a duniya zai iya rage shigowar jari zuwa kasashe masu tasowa kamar Najeriya.
Na uku kuma shi ne hanyar samar da kayayyaki a duniya, inda matsalolin hanyoyin jiragen ruwa ko hanyoyin makamashi za su iya kara kudin sufuri da farashin kayayyaki a cikin gida.
Gwamnati ta kuma yi gargadin cewa idan rikicin ya dauki lokaci mai tsawo, zai iya kara matsin hauhawar farashi da tsadar rayuwa idan farashin kayayyaki a duniya ya ci gaba da tashi.
Ministan kudi, Wale Edun ya ce irin wannan rashin tabbas zai iya jawo karin farashin kayayyaki da ayyuka, wanda zai kara matsin hauhawar farashi da tsadar rayuwa ga 'yan Najeriya.
Yakin Iran da Isra'ila ya taɓa Dangote
An ji cewa a karo na uku cikin mako guda, matatar Dangote ta kara farashin litar man fetur a wuraren da take ba yan kasuwa sari a Najeriya.
Wannan kari da ake yawan samu a bayan bayan nan na da nasaba da yakin Iran da Amurka/Isra'ila, wanda ya jawo tashin danyen mai a duniya.
Kungiyar PETROAN ta yi hasashen cewa idan ba a dakatar da wannan yaki ba, farashin fetur zai iya kai wa N2,000 a Najeriya.
Asali: Legit.ng
