Ta Leko Ta Koma: Kasashe Sun Ki Karbar Jakadun Najeriya da Tinubu Ya Tura

Ta Leko Ta Koma: Kasashe Sun Ki Karbar Jakadun Najeriya da Tinubu Ya Tura

  • A ranar 6 ga watan Maris 2026 shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kasashen da ya tura jakadu da za su zama wakilan Najeriya
  • Sai dai kasa da mako daya da sanar da kasashen da aka tura jakadun, kasashe sun fara nuna shakku game da karbar su saboda wasu dalilai
  • Tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, tsofaffin ministoci da jami'an tsaro na cikin wadanda shugaban kasar ya tura kasashen duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Indiya da wasu kasashe da ba a bayyana sunayensu ba sun ki amincewa da wasu daga cikin jakadun da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada kwanan nan.

Wasu manyan jami’ai a fadar shugaban kasa da kuma ma’aikatar harkokin waje sun bayyana cewa Indiya, tana da wata doka da ta dade tana bi wadda ke hana karbar jakadu bisa wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Iran ta bukaci kasashe su fatattaki jakadun Amurka da Isra'ila

Shugaba Bola Tinubu a ofis
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tagumi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch da ta fitar da rahoton ta wallafa cewa gogaggen jami’in diflomasiyya, Ambasada Muhammad Dahiru shugaba Tinubu ya tura kasar Indiya.

An ki karbar jakadun Tinubu

An samu labarin cewa kasar Indiya na amfani da ikon da take da shi na kin amincewa da bukatar ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karbi Muhammad Dahiru a matsayin jakada.

Hakan ya tabbatar da wani rahoto da Legit ta wallafa tun a watan Fabrairu na shekarar 2026, inda wasu majiyoyi suka bayyana cewa wasu daga cikin jakadun da Tinubu ya nada na iya fuskantar kin amincewa daga kasashen da za su je aiki.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Bola Tinubu na magana a jihar Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Majiyoyin da suka bukaci a boye sunayensu saboda muhimmancin tattaunawar diflomasiyya, sun ce gwamnatin tarayya ta riga ta fara samun sakonni daga New Delhi da ma wasu manyan kasashe cewa ba su da niyyar karbar jakadu.

Dalilan kin karbar jakadun Najeriya

Dangane da dalilan kin karbar jakadun Najeriya da Bola Tinubu ya tura, wani jami’i a fadar shugaban kasa ya ce:

Kara karanta wannan

Gbajabiamila da yaran Tinubu da suka rike amana yau ake damawa da su a gwamnati

“Ba sa karbar jakada daga gwamnatin da wa’adinta ya rage kasa da shekara biyu. Don haka tuni suke nuna mana irin wannan alama.”

The Sun ta rahoto ya ci gaba da cewa:

“Wasu kasashe na jin shakku wajen karbar wasu mutane, ba wai saboda mutanen ba ne, saboda lokaci ne. Sun riga sun fara kallon gwamnatin Tinubu a matsayin gwamnati mai shirin barin gado.
“Don haka damuwarsu ita ce saura shekara daya da kadan kacal gare shi, me zai faru idan bai sake lashe zabe ba? Wata gwamnati na iya zuwa ta sauke su.

Majiyar ta jaddada cewa duk da cewa Indiya ce kadai aka tabbatar tana da irin wannan doka kan jakadu masu gajeren wa’adi, wasu kasashe ma na iya bin irin wannan al’ada.

Tinubu ya tura jakadu kasashe

A wani labarin, kun ji cewa a ranar Juma’a, 6 ga Maris, 2026 shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin jakadu zuwa kasashe daban-daban da kuma majalisar dinkin duniya.

Daga cikin mutane 65 da aka nada akwai tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode, wanda nadinsa ya jawo ce-ce-ku-ce.

Laftanar Janar Abdulrahman Dambazzau (Mai ritaya) da Sanata Jimoh Ibrahim na cikin mutanen da shugaba Bola Tinubu ya tura kasashen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng