A Karon Farko bayan Fara Yakin Iran da Amurka, Dangote Ya Tausaya Wa 'Yan Najeriya
- A karon farko bayan tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, matatar Dangote ta rage farashin fetur da dizal ga yan kasuwa
- Matatar ta sanar da ragin N100 a farashin sari na kowace litar fetur, da rangwamen N190 a kan kowace litar dizal a fadin Najeriya
- Wannan rangwame na iya zama hanyar rage radadi ga 'yan Najeriya duba da yadda farashin ya yi ta tashi a kwanakin baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legas, Nigeria - Yayin da yakin Amurka, Isra'ila da Iran ke kara haifar da matsin tattalin arziki a duniya, matatar Dangote ta tausayawa 'yan Najeriya, ta rage farashin fetur da dizal.
Hakan na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa gangar danyen mai ta sauka a karon farko a kasuwar duniya bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya a karshen watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Source: Getty Images
Matatar Dangote ta yi rangwamen N100
A rahoton da Tribune Nigeria ta wallafa yau Talata, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur (PMS) da Naira N100,
Bisa ga sabon jadawalin farashin da matatar ta fitar a ranar 10 ga Maris, 2026, an rage farashin man fetur daga N1,175 zuwa N1,075 kan kowace lita a wurin bada sari ga 'yan kasuwa.
Haka kuma, matatar ta bayyana cewa farashin man fetur ga masu jigilar kaya ta ruwa zai kasance N1,050 kan kowane lita.
Takaitaccen bayanin sabon farashin
Nau'in mai | Farashin da | Sabon farashi | Rangwamen da aka samu |
Man fetur | N1,175 | N1,075 | N100 |
Man Dizal | N1,620 | N1,430 | N190 |
Matatar ta Dangote ta kuma yi karin bayani da cewa wadannan farashin ba su hada da kudaden haraji na hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA ba.
Yadda fetur ya yi tsada a mako 1
Tun da fari, jaridar Punch ta ruwaito cewa matatar Dangote ta kara farashin man fetur zuwa N1,175 a ranar Litinin, wanda shi ne karo na uku da aka samu karin farashin a cikin kwanaki bakwai.
Matatar ta sanar da sabon farashin ga masu sayarwa da masu gidajen mai a ranar Litinin, inda aka samu karin N180 daga N995 zuwa N1,175.

Source: Getty Images
Hakan ya nuna an samu karin kashi 18.1 a cikin kwanaki uku kacal kafin wannan sabon rangwamen na yau Talata.
Wannan ragin farashin na iya zama wani mataki na rage radadi ga 'yan Najeriya duba da yadda farashin ya yi ta tashin gwauron zabi a kwanakin baya.
PETROAN ta yi hasashen tashin farashin fetur
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta PETROAN ta yi gargadin cewa farashin fetur zai kara hauhawa daga yadda ya ke a yanzu.
Lamarin ya biyo bayan yaki da ake kan yi tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran da aka shafe akalla kwanaki 10 ana gwabzawa a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry ya nuna fargaba cewa farashin litar fetur zai iya tashi har zuwa kusan ₦2,000 yayin da dizal zai doshi N3,000.
Asali: Legit.ng
