Gwamna Ya Kunyata a Kotu da Ya Nemi Alkali Ya ba Shi Damar Rantsar da Shi Sau 3 a Mulki

Gwamna Ya Kunyata a Kotu da Ya Nemi Alkali Ya ba Shi Damar Rantsar da Shi Sau 3 a Mulki

  • Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan karar da Gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya shigar a gabanta
  • A hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke, ta amince da wanda babbar kotun tarayya da ke Akure ta yanke kan shari'ar Aiyedatiwa
  • Hakazalika, kotun daukaka karar ta kuma ci gwamnan tarar kudi, tare da ba shawarar ya je kotun gaba idan bai gamsu da hukuncin ba

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya shigar a gabanta.

Gwamna Aiyedatiwa ya shigar da karar ne yana ƙalubalantar hukuncin babbar kotun tarayya da ke Akure a wata ƙara da ke tantance cancantarsa ta sake tsayawa takarar zaɓen gwamna mai zuwa a jihar.

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar Gwamna Lucky Aiyedatiwa
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce kotun ta yanke hukunci ne yayin zamanta na ranar Litinin, 9 ga watan Maris na shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Kotun daukaka kara ta raba gardama kan rikicin jam'iyyar PDP

A cikin wani hukunci na bai-ɗaya da kwamitin alkalai mutum uku ya yanke, kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke cewa kotun farko ta yi amfani da hikimarta yadda ya kamata lokacin da ta amince da buƙatar mai shigar da kara, Dr. Akindele Egbuwalo.

Gwamnan Ondo ya yi rashin nasara a kotu

Egbuwalo, wanda jigo ne a jam’iyyar APC a Jihar Ondo, ya shigar da ƙara a babbar kotun yana neman fassarar sashe na 137(3) na kundin tsarin mulki dangane da cancantar Aiyedatiwa da mataimakinsa, Dr. Olayide Adelami, na tsayawa takara a karo na biyu.

A cikin wani hukunci na ranar 24 ga Nuwamba, 2025, mai shari'a Toyin Adegoke ta babbar kotun tarayya da ke Akure ta amince da buƙatar mai ƙaran na yin gyara ga takardun ƙarar

Shari'a ya kai Gwamna Aiyedatiwa kotun daukaka kara

Sakamakon rashin gamsuwa da wannan hukunci, Gwamna Aiyedatiwa ya shigar da ƙara a kotun ɗaukaka ƙara, inda ya yi zargin cewa an saba wa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki na samun shari’a ta adalci.

Ya yi iƙirarin cewa alƙalin kotun farkon ta yi abin da ya fi ƙarfin ikonta kuma ta karɓi hurumin shari’ar ta hanyar kuskure.

Kara karanta wannan

Ana jiran hukuncin babbar shari'ar da za ta bayyana makomar jam'iyyar PDP

Sakamakon iƙirarin na Aiyedatiwa, kotun daukaka kara da ke Akure, inda aka fara shigar da maganar da farko, ta umarci babbar kotun da ta dakatar da shari’ar, wadda tuni aka riga aka sanya ranar yanke hukunci a kanta.

Wane hukunci kotu ta yanke?

Yayin da yake karanta hukuncin, Mai shari'a Uchechukwu Onyemenam ya yanke hukuncin cewa Aiyedatiwa ya gaza nuna cewa hukuncin da babbar kotun ta yanke na ba da damar yin gyaran fuska ya haifar da wani rashin adalci ko kuma ya hana shi hakkinsa na samun shari’a ta adalci.

Sakamakon haka, kotun ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da ƙarar saboda rashin hujjoji, sannan ta ci tarar gwamnan N2m, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Hukuncin ya tabbatar da matsayar ranar 24 ga Nuwamba, 2025, ta babbar kotun tarayya da ke Akure, wadda ta ba Egbuwalo damar yi wa ƙararsa gyaran fuska a cikin shari'ar da yake ƙalubalantar cancantar Aiyedatiwa na sake tsayawa takara.

Tun da fari a lokacin shari'ar, kotun daukaka ƙara ta kuma yi watsi da wata buƙata da Aiyedatiwa ya shigar, yana neman a soke wani umarni da ta bayar ranar 27 ga Janairu, 2026, na dakatar da ci gaba da shari’ar a gaban babbar kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Kotu ta ci tarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa
Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa na jihar Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Source: Facebook

Kotu ta ba Aiyedatiwa shawara

Kotun ta bayyana cewa zaɓin da ya rage wa gwamnan shi ne ya ƙalubalanci wannan hukunci a gaban Kotun Koli.

Daga baya kwamitin alkalan kotun ya umarci Lucky Aiyedatiwa da ya biya ƙarin Naira miliyan biyu (N2m) a matsayin kuɗin shari’a.

Mai girma Aiyedatiwa ya zama gwamna ne a sakamakon mutuwar marigayi Rotimi Akeredolu a 2023.

Hadiman Gwamna Aiyedatiwa sun ajiye aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin hadiman Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, sun ajiye mukamansu.

Hadiman guda biyu na Gwamna Aiyedatiwa sun yi murabus daga mukamansu na mataimaka na musamman a fannin yaɗa labarai.

Hadiman sun nuna godiyarsu ga Gwamna Aiyedatiwa saboda damar da ya ba su ta yin aiki a cikin gwamnatinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng