Kasar Iran Ta Fasa Kwai, Ta Fadi Dalilin Amurka da Isra'ila Na Kai Mata Hari

Kasar Iran Ta Fasa Kwai, Ta Fadi Dalilin Amurka da Isra'ila Na Kai Mata Hari

  • Yankin Gabas ta Tsakiya ya tsinci kansa cikin rikici sakamakon yakin da Amurka da Iran suka kaddamar a kan kasar Iran
  • Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya bayyana manufar da Amurka da Isra'ila ke son cimmawa sakamakon kai hare-haren
  • Gholamreza Mahadavi Raja ya bayyana cewa hare-haren na Amurka da Isra'ila na shafar fararen hula a kasar Iran

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya zargi Amurka da yin amfani da rikicin da ake yi da Iran a halin yanzu domin ta samu ikon sarrafa arzikin makamashi na kasar.

Gholamreza Mahdavi Raja ya bayyana ayyukan gwamnatin Amurka a matsayin waɗanda “burin mamaya” ke tunzura su.

Iran ta zargi Amurka da kokari kwace man fetur dinta
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Jakadan na Iran a Najeriya ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Daily Politics na tashar Trust Tv ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Tofa: Rigima ta barke tsakanin Amurka da Isra'ila kan yaki da Iran, an ji dalilin sabanin

Me Jakadan Iran ya ce kan Amurka, Isra'ila?

Gholamreza Mahdavi Raja ya ce hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran kwanan nan wani ɓangare ne na babban shirin su na mamaye arzikin man fetur na Iran.

“Babban burin Amurka da gwamnatin Isra'ila na wannan zalunci shi ne su ƙwace arzikin makamashin Iran. Gwamnatin Isra'ila tana son ganin rugujewar Iran, su da kansu ne suka sanar da hakan."

- Gholamreza Mahdavi Raja

Duk da hare-haren da aka kai wa ababen more rayuwa, Raja ya ce gwamnatin Iran tana ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, kuma al’ummar Iran sun kasance tsintsiya madaurinki ɗaya wajen kare ikon ƙasarsu.

Batun zaben sabon jagoran Iran

Jakadan ya kuma yi watsi da duk wani tasiri na waje wajen zaɓar sabon Jagoran Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ɗan marigayi Ayatollah Khamenei, inda ya jaddada cewa:

"Iran ƙasa ce mai cin gashin kanta. Muna yanke shawarwarinmu ne ba tare da tsoma bakin wasu daga waje ba.”

Kara karanta wannan

Hezbollah ta kakkabo jirgin yaƙin Isra'ila, an kashe fiye da mutane 1330 a Iran

Hare-haren Amurka, Isra'ila na barna a Iran

Game da tasirin yaƙin ga jama'a, jakadan ya zargi makaman Amurka da sauka a wuraren fararen hula, ciki har da wata makaranta a birnin Minab, inda ya yi iƙirarin cewa an kashe yara da dama.

Ya dage kan cewa Iran tana kai hari ne a sansanonin sojoji ne kawai a yankin Gulf, sannan ya zargi Washington da Isra’ila da shirya “makircin ɓoye” domin ɗora wa Tehran laifi.

Iran ta zargi Amurka da kai hari kan fararen hula
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Batun daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Haka kuma Raja ya yi watsi da iƙirarin Isra’ila na cewa Iran tana ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya, inda ya bayyana hakan a matsayin zargi mara tushe kuma mai nasaba da siyasa.

Jakadan ya jaddada cewa dangantakar Iran da kungiyar harkar Musulunci ta Najeriya ta shafi addini da al'ada ce kawai.

Sanatocin Amurka na son a yi bincike

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sanotocin jam'iyyar Democrat na son gwamnatin Amurka ta gudanar da bincike kan wani harin da ake zargin dakarunta sun kai a Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta kada hantar Isra'ila, ta fadi tsawon lokacin da za ta yi tana yakarta

Sanatocin sun yi kiran da a gudanar da bincike kan harin da aka kai wa wata makarantar yara mata a Kudancin Iran wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 170.

Manyan sanatocin sun bayyana cewa dole ne ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta ba da cikakkun amsoshi game da lamarin wanda ya jawo asarar rayukan fararen hula.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng