Arzikin Abdussamad ya ninku 2, ya doke mutane ya zama attajiri na 3 a Afrika
- Aliko Dangote ya ci gaba da zama mutum mafi arziki a Afrika yayin da dukiyar attajiran nahiyar ta karu sosai a shekarar da ta gabata
- Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa dukiyar attajiran Afrika 23 ta karu zuwa Dala biliyan $126.7 a shekarar da ta gabata
- Abdulsamad Rabiu ya samu mafi girman karin dukiya a jerin bayan yawan kadararsa ya tashi da kashi 120%
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Rahoton sabon jerin masu kudin duniya ya nuna cewa attajiran Afrika sun kara karfi a bangaren yawan dukiya.
Rahoton da aka fitar a wannan shekara ta 2026 ya nuna cewa wasu daga cikinsu sun samu karin biliyoyin Daloli a cikin shekara guda.

Kara karanta wannan
Yakin Iran da Amurka ya kara taba Dangote, ya canza farashin fetur karo na 3 a Najeriya

Source: Facebook
The Cable a wallafa cewa a cewar rahoton, hamshakin attajirin Najeriya kuma wanda ya kafa kamfanin Dangote, Aliko Dangote, yana cigaba da rike matsayin mutum mafi arziki a Afrika.
Yadda dukiyar Dangote da AbdulSamad ta karu
Channels TV ta wallafa cewa rahoton da mujallar Forbes a fitar ya bayyana cewa dukiyar attajiran Afrika guda 23 ta karu da Dala biliyan 20.3 a cikin shekara daya kacal.
Wannan karin ya kai kusan 21% idan aka kwatanta da shekarar 2025. Dangote ya samu karin dukiya sosai, inda jimillar dukiyarsa ta kai Dala biliyan $28.5.
Wannan ya biyo bayan tashin darajar hannayen jarin kamfanin siminti da kusan 69% tun daga watan Maris na shekarar 2025.
Baya ga haka, kamfanin ya kuma sanar da samun ribar da ta kai Naira tiriliyan daya a shekarar 2025, abin da ya kara karfafa matsayinsa a jerin attajiran nahiyar.

Source: Getty Images
Abdussamad Rabiu ya mallaki N15tr
Rahoton ya kuma nuna cewa shugaban rukunin kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, shi ne ya fi kowa samun karin dukiya a jerin.
Dukiyarsa ta karu da 120% wato kusan Dala biliyan 6.1, inda jimillar dukiyarsa ta kai Dala biliyan 11.2.
A sakamakon ribanyar da arzikinsa ya yi a cikin shekara guda, Alhaji Abdussamad Rabiu ya samu N8.3tr kuma dukiyarsa a yau a lissafin Dala ta kai N15.5tr.
Wannan karin dukiya ya daga AbdulSamad Rabiu daga matsayi na shida zuwa na uku a cikin jerin attajiran Afrika.
A yanzu yana bayan hamshakin attajirin Afirka ta Kudu, Johann Rupert, wanda ya rike matsayi na biyu da dukiyar Dala biliyan $16.1.
Sauran attajiran Najeriya a jerin Forbes
A matsayi na hudu kuwa akwai Nicky Oppenheimer da iyalinsa, wadanda dukiyarsu ta kai Dala biliyan 10.6, bayan da ta karu da kusan Dala miliyan 200 daga Dala biliyan 10.4 a watan Afrilu na 2025.
Dan kasuwar Masar, Nassef Sawiris, wanda ke da hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa F.C. kuma yake da kusan kashi 6% a kamfanin Adidas, shi ne na biyar mafi arziki a Afrika da $9.6bn.
Daga cikin ‘yan Najeriya da suka shiga jerin akwai wanda ya kafa Globacom, Mike Adenuga, wanda ya zo matsayi na shida da $6.5bn, bayan ya sauka daga matsayi na biyar a bara.
Haka kuma shugaban First HoldCo, Femi Otedola, ya sauka zuwa matsayi na 22 da dukiyar da $1.3bn, daga matsayi na 16 da yake a baya.
Dangote ya shirya bunkasa arzikinsa
A baya, mun wallafa cewa fitaccen attajirin dan kasuwa a Afrika, Aliko Dangote, na shirin fadada harkokin kasuwancinsa zuwa wasu fannoni daban-daban.
Dangote na shirin shiga fannin samar da wutar lantarki da karafa don bunkasa samar da masana'antu a nahiyar Afrika da kara fadada kasuwancinsa daga yadda ya ke a yanzu.
Babban dan kasuwar ya kuma bayyana cewa ana shirin kara fadada matatarsa mai tace gangar mai 650,000 a kowace rana Read more:
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

