Shiri Ya Baci: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Babban Kwamandan Sojoji a Borno
- 'Yan ta'addan Boko Haram dauke da miyagun makamai sun sake kai harin ta'addanci a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
- Tsagerun 'yan ta'addan sun farmaki wani sansanin sojojin Najeriya inda suka tafka gagarumar barna bayan sun yi artabu da jami'an taaro
- Sabon harin na 'yan ta'addan Boko Haram na zuwa ne bayan sun kai wani makamancinsa a wani sansanin sojoji da sansanin 'yan gudun hijira
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - ’Yan ta’addan Boko Haram sun mamaye wani sansanin sojojin Najeriya a jihar Borno.
'Yan ta'addan na Boko Haram sun kashe babban kwamandan rundunar (CO) da wasu jami’an sojojin Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa sabon harin ya faru ne a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno a farkon ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026.
'Yan Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji
Wata majiya daga garin ta bayyana cewa maharan sun kai hari kan sansanin sojojin ne da misalin karfe 12:30 na dare.
“Su (’yan ta’addan) sun farmaki garin ne ta fuskoki daban-daban sannan suka ƙaddamar da hari kan sansanin sojoji.”
- Wata majiya
Wata majiyar tsaro ta daban ta ce maharan sun fatattaki dakarun sojoji daga sansanin, suka ƙona motoci tare da kwashe makamai da albarusai, jaridar TheCable ta kawo labarin.
“Ba zan iya cewa uffan game da yawan mutanen da aka kashe ba, amma abin baƙin ciki ne ƙwarai da muka rasa babban kwamandanmu (CO) a nan."
- Wata majiyar tsaro
Sun taba kai hari a sansanin
A watan da ya gabata, maharan sun kai hari a sansanin sojojin amma jaruman dakarun sun dakile harin, inda suka kashe ’yan ta’adda da dama.
Al’ummar garin sun yaba wa wannan jarumta da aka nuna, wanda hakan ya sa babban kwamandan ya samu yabo kuma aka yi ta murnar nasararsa, musamman a kafofin sada zumunta.
Ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Kukawa a majalisar dokokin jihar Borno, Karta Maina Ma’aji Lawan, shi ma ya taya dakarun murna a wancan lokacin.

Source: Original
Dan majalisa ya koka kan harin Boko Haram
Yayin da yake tsokaci kan sabon harin, ɗan majalisar ya ce abin baƙin ciki ne yadda aka mamaye sansanin sojojin a wannan karon.
Harin ya zo ne bayan da ’yan ta’adda suka kai hari wani sansanin sojoji da sansanin ’yan gudun hijira a garin Ngoshe, ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda suka kashe sojoji da fararen hula da ba a tantance yawansu ba.
Boko Haram ta kwace gari guda a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa mayakan kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram sun karbe iko a garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan sun yi awon gaba da mata da yara fiye da 100, sannan sun kashe sojoji da dama yayin harin da suka kai a garin.
Wani soja da ya tsira daga harin ya bayyana yadda ya ga ƴan ta'addan suna yanka abokan aikinsa kamar kaji bayan sun fi ƙarfin sojojin sakamakon yawansu da kuma miyagun makamai.
Asali: Legit.ng

