Kasar Muslunci ta Iran ta Nuna Sha'awar Taimakawa Najeriya Wajen Yaki da Ta’addanci
- Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya ce kasarsa a shirye take ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci
- Ya bayyana goyon bayan Iran ga Najeriya kan barazanar Boko Haram da ISWAP, yana mai Allah wadai da ta’addanci a ko wane irin salo
- Har ila yau jakadan ya yi watsi da zargin Isra’ila cewa Iran na da hannu a ta’addanci a Najeriya ta kowacce fuska
Birnin Tarayya, Abuja - Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya bayyana cewa Iran a shirye take ta taimaka wa Najeriya a kokarinta na yaki da ta’addanci.
Jakadan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar AriseTV a ranar 8 ga watan Maris, 2026, inda ya jaddada kudurin Iran na hada kai da gwamnatocin da ke fuskantar barazanar tsaro.

Source: Getty Images
“Iran na yin Allah wadai da ta’addanci a ko wane irin salo, kuma tana shirye ta hada kai da gwamnatocin da ke fuskantar irin wannan matsala.
“Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyoyin Boko Haram da ISWAP; don haka muna shirye don taimaka wa gwamnati wajen yakar ta’addanci. Mu ma Iran mun sha fama da ta’addanci, saboda haka muna Allah wadai da shi a Najeriya.”
Kalubalen tsaro a Najeriya
Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro daga kungiyoyin masu tayar da kayar baya kamar Boko Haram da ISWAP, wadanda suka jefa al’umma cikin rashin zaman lafiya a sassa da dama na kasar.
Maganar jakadan ta nuna cewa Iran na da niyyar bayar da gudummawa yayin da Najeriya ke neman karin hadin kai daga kasashen duniya domin tinkarar wadannan barazana.
Kasashe da dama na da alaka da Najeriya wajen yaki da abubuwan da suka shafi ta'addanci da rikicin kashe-kashe da sace mutane.
Iran ta yi martani ga zargin Isra’ila
Jakada Raja ya kuma yi magana kan zargin da jakadan Isra’ila a Najeriya ya yi cewa Iran na daukar nauyin ta’addanci a kasar.
Ya yi watsi da wannan zargi, yana mai cewa wani yunkuri ne na raunana dangantakar Najeriya da Iran wadda ta shafe fiye da shekaru sittin tana gudana.
Ya ce:

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya
“Zargin da jakadan Isra’ila a Najeriya ya yi cewa Iran na daukar nauyin ta’addanci a Najeriya na nufin lalata dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Iran wadda ta wuce shekaru sittin.
“Iran na girmama ikon Najeriya da tsaronta, kuma tana daraja dangantakarta da gwamnati da al’ummar kasar.
“Isra’ila kuwa a daya bangaren ta na da hannu wajen daukar nauyin ta’addanci da kashe-kashe a wasu kasashe, don haka irin wannan zargi wata dabara ce ta karkatar da hankali daga gaskiyar lamarin.”
Doguwar dangantaka tsakanin Najeriya da Iran
Najeriya da Iran sun dade suna hulda da juna tsawon sama da shekaru sittin, dangantakar da ta ginu kan mutunta juna da hadin kai.
A tsawon shekaru, kasashen biyu sun yi hulda a fannoni daban-daban da suka hada da kasuwanci, al’adu da kuma tsaro, abin da ya kara karfafa dangantaka tsakanin su.
Iran ta sha jaddada girmama ikon Najeriya da tsaronta, tana mai nuna kanta a matsayin abokiyar hulda wajen taimakawa wajen magance kalubale irin su ta’addanci.
Wannan dangantaka mai tsawo na nuna muhimmancin diflomasiyya da hadin kai tsakanin kasashen biyu, duk da matsin lamba ko suka daga wasu bangarori na duniya.
Asali: Legit.ng
