Iran Ta Faɗi Halin da Ƴan Najeriya ke ciki a Kasar yayin da Ake Ci Gaba da Ɓarin Wuta
- Jakadan Iran a Najeriya, Mahdavi Raja, ya yi magana kan halin da yan kasar ke ciki yayin da ake yaki tsakaninta da Isra'ila
- Raja ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran suna cikin koshin lafiya duk da rikicin Amurka, Isra’ila da Iran
- Ya ce babu wani rahoton cutarwa ga ‘yan Najeriya da ke birane kamar Tehran da Qom, yana mai jaddada matakan tsaron na kare kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jakadan Iran a Najeriya, Mahdavi Raja ya yi karin haske kan halin da yan kasar ke ciki yayin da ake tsaka da yaki.
Raja ya bayyana cewa yan Najeriya da ke zaune a can suna cikin koshin lafiya duk da rigimar da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Facebook
Raja ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Alhamis 5 ga watan Maris, 2026 a Abuja dangane da halin da ake ciki, cewar Vanguard.
Iran ta ba yan Najeriya tabbaci
Ya ce tun bayan fara rikicin soja tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, babu wani rahoto da ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun samu rauni a ƙasar.
Raja ya ce ‘yan Najeriya suna zaune lafiya a manyan biranen Iran kamar Tehran da Qom, kuma hukumomi suna kula da tsaron baki.
Ya jaddada cewa matakan da Iran ke ɗauka a rikicin na kare kai ne kawai domin kare yankinta da al’ummarta bisa dokokin ƙasa da ƙasa.
Ya ce tsaron baki da suka haɗa da ‘yan Najeriya na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bai wa muhimmanci.
Jakadan ya ce hare-haren da Iran ke mayarwa suna nufin wuraren soji ne kawai, ba sa barazana ga fararen hula ko baki da ke zaune a ƙasar.
Raja ya kuma bayyana cewa Iran za ta ci gaba da girmama dangantakar diflomasiyya da kuma tattaunawa da ƙasashe duk da kare ‘yancin ƙasarta.
Duk da halin da ake ciki, ya ce tsaro da jin daɗin baki da ke zaune a Iran ba su samu wata matsala ba.

Source: Twitter
Rokon Iran ga yan Najeriya a kasar
Jakadan ya roƙi ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje su kwantar da hankula tare da bin umarnin hukumomi domin kare lafiyarsu.
Ya kuma buƙaci ƙasashen duniya su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare da girmama haƙƙin Iran na kare ƙasarta.
Wannan bayani na jakadan ya zo ne yayin da gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ido kan halin da ake ciki a Iran da ƙasashen yankin Gulf, cewar The Nation.
Gwamnatin Najeriya ta fitar da shawarwarin tafiya ga ‘yan ƙasar da ke Iran da ƙasashen makwabta domin su kula da tsaro.
Haka kuma Hukumar ‘Yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, NiDCOM, ta ce tana aiki tare da hukumomi domin tallafa wa ‘yan Najeriya da ke yankin.
Najeriya ta yi magana kan yakin Iran, Isra'ila
A baya, Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadin tsaro ga ’yan Najeriya mazauna Iran da kasashen Gulf ana tsaka da rigima.
Wannan sanarwa ya biyo bayan kai hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran da ya tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce tana sa ido kan rikicin da ke kara kamari, tare da shawartar jama’a su guji wuraren sojoji da taruka.
Asali: Legit.ng


