'Yan Bindiga Sun Shammaci 'Yan Sanda Ana Azumi, Sun Yi Barna Mai Girma

'Yan Bindiga Sun Shammaci 'Yan Sanda Ana Azumi, Sun Yi Barna Mai Girma

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa bayan da suka farmaki jami'an 'yan sanda a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindiga wadanda suka kasance masu dumbin yawa, sun yi harbe-harbe kan mai uwa da wabi bayan da suka farmaki jami'an 'yan sandan
  • Harin da 'yan bindiga suka kai a wani shingen bincike ya jawo an samu asarar rayukan jami'an 'yan sanda tare da kona kayan da suke amfani da su

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe jami’an ’yan sanda biyu a jihar Kebbi.

'Yan bindigan sun kashe 'yan sandan ne yayin wani hari da suka kai kan shingen binciken ababen hawa a karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Ana yakin Iran da Amurka, 'yan Boko Haram sun kashe kwamandan sojoji, sun yi barna

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Kebbi
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun far wa shingen ’yan sandan ne da ke kan hanyar kan iyaka ta Bakin Ruwa zuwa Maje, inda suka buɗe wa jami’an da ke gadin wurin wuta.

'Yan bindiga sun shammaci 'yan sanda

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun zo ne da dumbin yawa, sannan suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar jami’ai biyu da ke bakin aiki.

Bayan harin, maharan sun kuma ƙone tantin da jami’an ke amfani da shi a wurin binciken, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Wani mazauna yankin ya bayyana cewa maharan sun fi ƙarfin jami’an saboda yawan da suke da shi, inda suka gudanar da harin sannan suka tsere daga wurin.

Me 'yan sanda suka ce kan harin?

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce an kashe jami’ai biyu lokacin harin.

Kara karanta wannan

Masu mu'uzijar karya: An cafke malaman addini 6 da ke damfarar mutane a Najeriya

“Sun kashe jami’anmu biyu kuma sun kone shingen binciken, amma rundunar tana nan tana kokarin shawo kan lamarin. Zan bayar da karin bayani nan gaba."

- Bashir Usman

'Yan bindiga na kai hare-hare a Kebbi

Wannan shi ne hari na uku da aka kai wa jami’an tsaro a kan hanyar kan iyaka ta Bakin Ruwa zuwa Maje.

'Yan bindiga sun kai hari kan 'yan sanda a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A wani hari da aka kai a baya a wannan yankin, an bayar da rahoton kashe jami’in ɗan sanda guda ɗaya.

Haka zalika, ’yan watanni da suka gabata, an kashe jami’an hukumar kwastam da na hukumar shige da fice su biyar a wani hari da aka kai a kan hanyar Maje a karamar hukumar ta Bagudo.

'Yan bindiga sun sace masallata

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani masallaci a jihar Kaduna lokacin da mutane ke gudanar da Sallar Tarawihi.

'Yan bindigan sun sace mutane shida yayin da suke gudanar da sallar tarawihi a cikin wani masallaci da ke yankin Azara na karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Tsagerun 'yan bindigan sun kutsa cikin masallacin tare da harbe-harbe kafin su yi awon gaba da mutane shida da suka hada da maza hudu da mata biyu. Rea

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng