Babban Basarake a Najeriya Ya Shiga Batun Yakin Amurka da Iran, Ya Aika Sako ga Trump

Babban Basarake a Najeriya Ya Shiga Batun Yakin Amurka da Iran, Ya Aika Sako ga Trump

  • Babban basarake a jihar Osun, Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi magana kan yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Oba Abdulrosheed Akanbi ya haska kuskuren da Donald Trump ya yi wajen goyon bayan Isra'ila ta farmaki kasar Iran
  • Basaraken ya bayyana cewa Amurka ta zubar da kimarta, kuma tabbas yakin ba zai haifar mata da abu mai kyau ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Oluwo na Iwo da ke jihar Osun, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi magana kan yakin Amurka da Iran.

Oba Abdulrosheed Akanbi ya kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump, da ya nemi gafarar ƙasar Iran saboda nuna son goyon baya ga Isra’ila a yaƙin da ake yi tsakanin ƙasashen biyu.

Oluwo na Iwo ya soki Donald Trump
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi da Shugaba Donald Trump Hoto: Taofeek Adeniyi, Donald J. Trump
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce babban basaraken ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Osogbo ranar Laraba, 4 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Sarkin Iwo ya ce kan yakin Amurka-Iran?

Babban basaraken ya bayyana yaƙin na yanzu a matsayin "marar amfani", inda ya ce kashe jagoran Iran mai shekaru 86, Ayatollah Ali Khamenei, babban zunubi ne.

“Ina shakka ko Shugaban Amurka, Donald Trump, yana da tarihin mutumin da suka kashe. Ina addu’ar hakan ta kare da alheri."
"Ƙasashe matsorata ne kawai za su iya miƙa wuya ga irin salon da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi amfani da shi."

- Oba Abdulrosheed Akanbi

Basaraken ya yaba da jarumtar kasar Iran

Sarkin ya tunatar da cewa tsawon shekaru an sanya wa Iran takunkumi amma ta tsira, inda ya jaddada cewa wannan matsin lamba da Amurka ke yi wa Iran ba shi da wani amfani.

"Harba bama-bamai da aka yi wa Iran da kuma martanin da ta mayar tuni suka fara yin tasiri sosai ga tattalin arziƙin duniya. Fasinjoji da dama sun makale, kuma an rufe filayen jiragen sama a yankunan da abin ya shafa."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Wasu dakarun Iran sun yi yunkurin kashe shugaban Amurka, Trump

“Iraniyawa sun tsaya tsayin daka. Sun yi magana da zuciya daya. Amurka, wadda ke iƙirarin ita ce mai ƙarfi kuma alkali, tana nuna son kai a wasan da ya kamata ta jagoranta a matsayin alƙali. Amurka ta rasa kimarta."
“Ya kamata a bar shugaban kowace ƙasa mai cin gashin kanta ya ji daɗin ’yancinsa. Kashe Ayatollah, shugaban Iran, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026, abin Allah wadai ne. Wanene ya san wa zai biyo baya?”

- Oba Abdulrosheed Akanbi

Oluwo na Iwo ya soki shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi Hoto: Taofeek Adeniyi
Source: Facebook

Wane sako sarkin ya ba Trump?

Yayin da yake bayyana cewa Amurka ta rasa ikonta na kasancewa babbar ƙasa, Oluwo ya ce a matsayinta na babbar ƙasa a duniya, bai kamata ta nuna son kai ba lokacin da ɓangarori biyu ke yaƙi, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

“Shigar Amurka ba tare da yin kiran a tsagaita buɗe wuta ba ya sa sun rasa ikon mallakar duniya. Wannan artabu ne da bai zama dole ba kuma za a iya kauce masa."
"Ina shakka ko hakan zai ƙare da kyau ga Amurka. Ina son Amurka da Isra'ila. Kamata ya yi Trump ya ba Iran da duniya baki ɗaya haƙuri. Lokaci bai ƙure ba na gyara kuskure."

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

- Oba Abdulrosheed Akanbi

Amurka ta nutsar da jirgin ruwan yakin Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta shammaci Iran ta hanyar nutsar mata da jirgin ruwan yaki a cikin teku.

Jirgin ruwan yakin Amurka mai tafiya a karkashin ruwa ya harba wani makami mai hadari da ya nutsar da jirgin ruwan yakin Iran.

Rahotanni sun nuna cewa akwai sama da mutane 180 da ke cikin jirgin lokacin da aka harba masa makamin mai hadari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng