Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo Ya Mutu a Najeriya? Bayanai Sun Fito

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo Ya Mutu a Najeriya? Bayanai Sun Fito

  • Cif Olusegun Obasanjo ya musanta labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani, wanda ya yi ikirarin cewa ya mutu
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa har yanzu yana raye, kuma ba zai mutu ba sai ya gama ayyukan da Allah Ya dora masa nauyin aiwatarwa
  • Obasanjo ya caccaki masu masa fatan mutuwa, yana mai jaddada cewa Allah da kansa zai hukunta masu hannu a yadda wannan labari na karya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya musanta jita-jitar da aka fara yadawa cewa ya yi bankwana da duniya.

A yan kwanakin nan ne aka fara yada wani rubutu da ke nuna cewa Obasanjo ya mutu, kuma kafin ya bar duniya ya rubuta wata takarda game da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun harbo jirgin Iran marar matuki a Sokoto? An samu bayanai

Obasanjo.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yana jawabi Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook

Da gaske Olusegun Obasanjo ya mutu?

A wani rahoto da Daily Trust ta wallafa yau Laraba, 4 ga watan Maris, 2026, Obasanjo ya yi fatali da wannan rubutu da ake yadawa a soshiyal midiya, inda ya tabbatar da cewa yana nan a raye.

Obasanjo ya fadi haka ne don mayar da martani ne kan wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta, musamman WhatsApp, wanda ke ikirarin cewa ya fitar da wata sanarwa ta karshe game da rayuwarsa.

A cikin rubutun da ke jikin sakon, an bayyana Obasanjo a matsayin mai shekara 84, alhali kuwa tsohon shugaban ya cika shekara 89 a ranar Alhamis. An haife shi ne a ranar 5 ga Maris, 1937.

Abin da Obasanjo ya ce kan mutuwa

Da yake jawabi a wurin taron cika shekaru 89 da haihuwarsa da aka gudanar a Abeokuta, Jihar Ogun, Obasanjo ya bayyana masu yada labarin a matsayin “marasa aikin yi.”

Kara karanta wannan

Trump ya fadi kwanakin da zai shafe yana gwabza yaki da Iran

Ya ce Allah ya ba shi tabbacin tsawon rai tare da ikon cika abin da aka dora masa, yana mai jaddada cewa duk wanda ke fatan akasin haka “Allah ne zai hukunta shi.”

A ruwayar Vanguard, Obasanjo ya ce:

“Kafin kammala jawabi na, ina so in ja hankalinku kan jita-jitar da wasu marasa aikin yi ke yadawa. Sun wallafa tare da yada wata takarda ta bogi suna danganta ta da ni, suna cewa na rubuta sanarwar mutuwata."
“Wannan burinsu ne, amma ba haka Allah Ya taara a gare ni ba. Allah ya tabbatar min cewa yana da sauran ayyukan da zan yi a duniya, kuma ya ba ni ikon yin su.
"Wadanda ke fatan akasin haka kuwa, Allah ne zai hukunta su da kansa.”
Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo a wani taro a jihar Ogun Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook

Obasanjo ya shirya kare kansa a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana shirinsa na zuwa kotu don bayar da shaida kan batun kwangilar Mambilla.

Shaidan EFCC, Umar Babangida wada ya bayyana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya ce Obasanjo ya ba shi tabbacin cewa a shirye yake ya zo ya iare kansa.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye gaban kotu kan aikin tashar mambilla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262