Kwamishina Ya Yi Murabus daga Mukaminsa a Kano, Ya Mika Takarda ga Gwamna Abba
- Hon. Umar Haruna Doguwa ya yi murabus daga kujerar kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Kano a ranar Litinin, 2 ga Fabrairu, 2026
- Gwamna Abba ya amince da murabus din kwamishinan, tare da yaba masa bisa gudummuwar da ya ba gwamnatinsa da al'ummar Kano
- Ya yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba, sannan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Kano za ta ci gaba da dora wa kan nasarorin ya samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - A ranar Litinin da ta shige, kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya mika takardar murabus daga mukaminsa a hukumance.
Kasa da sa'o'i 24 bayan haka, gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus din kwamishinan, inda matakin ya fara aiki daga ranar Talata.

Source: Facebook
Abba ya amince da murabus din kwamishina
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, wacce ya wallafa a Facebook.
Gwamna Abba ya bayyana wasu daga cikin alheran Hon. Doguwa tun da ya hau mukamin kwamishina, inda ya gode masa bisa jajircewa, biyayya da kwazon da ya nuna wajen yi wa al’umma hidima.
Doguwa ya fara rike kujerar kwamishinan ilimi ta jihar Kano, inda a karkashinsa ne aka ayyana dokar ta bace a bangaren ilimi, matakin da ya kawo sauki a harkar koyo da koyarwa.
Abba Gida Gida ya tuna da wannan lokaci, inda ya ce Doguwa ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da manufofi da sauye-sauyen ilimi gaba, kafin a mayar da shi Ma'aikatar Albarkatun Ruwa.
Manyan nasarori a ma’aikatar ruwa
A cewar gwamnan, cikin shekara guda da Hon. Doguwa ya jagoranci Ma’aikatar Ruwa, an samu gagarumin ci gaba wajen gyara ababen samar da ruwa tare da fadada samar da ruwan sha ga al’umma a sassa daban-daban na jihar.

Kara karanta wannan
APC ko ADC: Gwamna ya gaji da rikicin PDP, ya fara shirin sauya sheka don zaben 2027
Ya kara da cewa jagorancinsa ya taimaka wajen karfafa hukumomin da ke karkashin ma’aikatar da kuma inganta ayyuka daidai da burin gwamnati na samar da ruwa mai tsafta ga jama’a.

Source: Facebook
Gwamna ya yi wa Hon. Doguwa fatan alheri
Ya yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba, sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da dora wa kan nasarorin da aka samu a bangaren albarkatun ruwa.
Gwamna Abba ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta da kuma inganta jin dadin al'ummar jihar Kano.
Sakamakon haka, Gwamnan ya umarci kwamishinan Ilimi, Gwani Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, da ya kula da Ma'aikatar Ruwa har zuwa lokacin da za a nada sabon kwamishina.
An ba da hutun karamar Sallah a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Kano ta bada hutun Sallah ga makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da ke a fadin jihar.
Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta ayyana ranar Lahadi, 1 ga watan Maris, 2026, a matsayin ranar da za a fara hutun ƙaramar Sallah.
Gwamnati ta ba da umarnin cewa iyaye da masu lura da ɗaliban da ke makarantun kwana su kwashe yaransu tun daga safiyar ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairu, 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
