Ta Ci Taliyar Karshe: Wike Ya Fadi Sanatar da Ba Zata Koma Kujerarta Ba a 2027

Ta Ci Taliyar Karshe: Wike Ya Fadi Sanatar da Ba Zata Koma Kujerarta Ba a 2027

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake takalo fada tsakaninsa da Sanata Ireti Kingibe
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa Sanata Ireti Kingibe ba za ta iya komawa kan kujerarta ba ta wakiltar Abuja a majalisar dattawan Najeriya
  • Ministan ya zayyano hujjojinsa da suka sanya yake ganin sanatar wadda ba sa ga maciji ba za ta kai labari ba a 2027

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake yin magana kan Sanata Ireti Kingibe.

Wike ya jaddada cewa Ireti Kingibe ba za ta koma majalisar dattawa ba a shekarar 2027, saboda a cewarsa, "ba ta da wani aikin da za ta nuna" wanda ta yi wa mutane.

Wike ya ce Kingibe za ta fadi zaben 2027
Sanata mai wakiltar Abuja, Ireti Kingibe da Nyesom Wike Hoto: Ireti Kingibe, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

Sanata Ireti Kingibe da Wike na takun saka

Sanata Kingibe, wadda ke wakiltar birnin Abuja a majalisar dattawa, an zaɓe ta ne a ƙarƙashin jam’iyyar LP shekarar 2023 amma daga bisani ta koma ADC.

Tun a shekarar 2024, Wike ya lashi takobin cewa ba za a sake zaɓar sanatar ba a zaɓe mai zuwa.

Kafin wannan lokacin, Kingibe ta yi iƙirarin cewa Wike ya ƙi amsa wasiƙu da saƙonnin da take tura masa dangane da ƙaruwar rashin tsaro a Abuja.

Sanatar ta kuma bayyana cewa Wike ba ya kishin mazauna Abuja a ransa, inda ta ce mazauna birnin na fama da ƙarancin ruwan sha da sauran ƙalubale.

Wannan ba shi ne karon farko da sanatar da ministan suke yin karan-tsaye da juna ba.

A shekarar 2024, Ireti Kingibe ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafka "babban kuskuren siyasa" wajen naɗa Nyesom Wike a matsayin Ministan Abuja.

Kwanan nan ma, sanatar ta soki Wike, tana mai cewa ya ƙi amsa saƙonnin da ta tura masa kan batun tsaro.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda APC ta yi kaca kaca da ƴan adawa a zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

Wike ya soki Sanata Ireti Kingibe
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Me Wike ya ce kan Sanata Ireti Kingibe?

Yayin da yake jawabi a wurin ganawa da manema labaran, Wike ya danganta hasashensa na cewa Kingibe ba za ta yi nasara ba da batun gaza samar da ayyukan ci gaba.

Ministan na Abuja ya bayyana sanatar ba ta da wani aiki da zai nuna wanda ta yi wa jama'ar da take wakilta, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

“Na faɗi hakan tun sama da shekara guda da ta gabata, Sanata Ireti, ba za ki dawo matsayin sanata ba."
"Shiyasa ku mutane ba ku son wanda yake gaya muku gaskiya. Gaskiya tana da ɗaci. Bari ta nuna aiki guda ɗaya da ta yi."

- Nyesom Wike

Ya ƙara da cewa Sanata Ireti Kingibe ba ta zuwa yankunan karkara na Abuja, inda a nan ne mutane suke fitowa da yawa don yin zaɓe.

Shugaba Tinubu ya yabawa Nyesom Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kwararo yabo ga Ministan babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Najeriya ta cire tsoro ta karyata rahoton Amurka kan Kiristoci

Tinubu ya yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa nasarorin da ya samu a Abuja wanda ya ce sun haifar wa APC ribar siyasa.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa kokarin da Wike ya yi a Abuja ya haifar wa APC ribar siyasa, duk da cewa ministan mamba ne na jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng