Yakin Iran: Arewacin Najeriya Ya Shiga Yankunan da ake Sa wa Ido

Yakin Iran: Arewacin Najeriya Ya Shiga Yankunan da ake Sa wa Ido

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi magana game da yanayin tsaron kasa yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Iran da Isra'ila/Amurka
  • Mukaddashin sufeto janar na ’yan sanda, Olatunji Disu ya umarci dakarunsa da su kara sa'ido domin tabbatar tsaro dukkan sassan Najeriya
  • Olatunji Disu ya bukaci bayar da kulawa ta musamman ga wasu yankunan Arewacin Najeriya domin tabbatar da komai ya tafi lafiya yayin rikicin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mukaddashin sufeto janar na ’yan sanda, Olatunji Disu ya umarci dukkan kwamishinonin ’yan sanda 37 na jihohi da babban birnin tarayya da su ƙara tsaurara sa ido a fadin ƙasar.

Ya bukaci kwamishinonin su mai da hankali musamman kan yankunan Arewa sakamakon abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya da suka samo asali daga rikicin duniya tsakanin Amurka/Isra’ila da Iran.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

Mukaddashin Sufeton 'yan sandan Najeriya
Mukaddashin sufeton 'yan sanda, IGP Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Disu, wanda ya yi magana ta bakin kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, a cikin wata sanarwa da ya fitar a X, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda da su ƙara sa ido da tattara bayanan sirri.

Za a kula da yankunan Arewa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sufeton 'yan sanda ya yi umarni da a kula da tsaron Najeriya, musamman Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma,

Umarnin shugaban ’yan sandan ya zo ne ’yan sa’o’i kaɗan bayan 'yan Shi'a sun gudanar da zanga-zangar lumana domin alhinin rasuwar jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Da yake mayar da martani, Disu ya umarci manyan jami’an ’yan sanda da su ƙara tabbatar tsaro a wuraren ibada da wuraren da jama'a ke taruwa.

Ya kara da bukatar a dakile duk wani yunƙuri na wasu mutane ko ƙungiyoyi na amfani da halin da ake ciki a duniya wajen haddasa rikici ko tayar da fitinar addini.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallata shi da shi a zaben 2027

Hundeyin ya ce:

“Mukaddashin IGP ya umarci dukkan kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da babban birnin tarayya, musamman a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya, da su ƙara sa ido da tattara bayanan sirri."
Ayatollah Ali Khamenei
Ayatollah Ali Khamenei da aka kashe a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Najeriya za ta tabbatar da tsaro

Rundunar ’yan sandan Najeriya na jaddada cewa Najeriya ba za ta zama filin rikicin ƙasashen waje ba kuma za a magance duk wani yunƙuri na shigo da rikicin akida ko na addini daga waje cikin ƙasar.

Ta ce:

“IGP Disu na kira ga shugabannin al’umma a fadin ƙasar da su ci gaba da inganta zaman lafiya, tare da roƙon ’yan ƙasa su kasance cikin natsuwa, a faɗake, kuma masu bin doka, su kuma kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
“Rundunar ’yan sandan Najeriya na nan daram, a shirye, kuma a dukkan lokuta tana jajirce wajen kare kowane ɗan Najeriya da tabbatar da tsaron ƙasa.”

Kara karanta wannan

Trump ya lallaba ya shiga Burkina Faso, ya ba Shugaba Traore miliyoyin daloli

Iran ta kai hari Isra'ila, kasashe

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Iran sun kai hare-hare kasashen duniya da Amurka ke da sansanin soji bayan farmakin da aka kai mata.

Hare-haren Iran ya shafi wani sansanin sojin Amurka a kasar Bahrain, inda aka hango hayaki na tashi a wajen bayan kamawa da wuta.

Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka, inda ya lalata wurare daban-daban a kasar Isra'ila da wasu yankunan Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng