Yan Bindiga Sun Sace Mahaifin Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya

Yan Bindiga Sun Sace Mahaifin Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi ta'asa bayan tabbatar da cewa sun sace Francis Igwe, mahaifin tsohon mataimakin gwamnan Ebonyi
  • Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci, inda ‘yan bindiga kan babur suka tare motarsa
  • Shugaban Ikwo, Sunday Nwankwo, da ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, suna cewa ana kokarin ceto dattijon cikin gaggawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abakaliki, Ebonyi — Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Francis Igwe, mahaifin tsohon mataimakin gwamnan Ebonyi, Dr. Kelechi Igwe.

Lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi 1 ga watan Maris, 2026 da muke ciki a garin Ndufu-Alike.

Yan bindiga sun dauke mahaifin tsohon mataimakin gwamna
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Majiyoyin Vanguard sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da Igwe ke tuki zuwa coci, inda wasu dauke da makamai kan babur suka tare shi.

Kara karanta wannan

Da gaske harin Iran ya hallaka Benjamin Netanyahu? an samu gaskiyar lamarin

Ana samun matsalolin tsaron a Ebonyi

Jihar Ebonyi na daga cikin jihohin a yankin Kudu maso Gabas a Najeriya da ke fama da matsalolin yan ta'adda wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Ko a kwanakin nan, an samu asarar rayukan al'umma duk da cewa ba harin yan bindiga ba ne wanda har gwamnan jihar da dauki mummunan mataki a yankin.

Gwamna Francis Nwifuru ya fusata matuka kan mummunan farmakin da aka kai kauyen Okporojo, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane hudu.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen garin Amasiri ne suka kai harin, saboda rikicin da ke tsakaninsu da kauyen Okporojo.

Gwamna Nwifuru ya tsige sarkin yankin tare da korar duk wani dan garin Amasiri da ke rike da mukami a gwamnatinsa.

Yan bindiga sun kashe dan siyasa a Ebonyi

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai farmaki ana tsaka da zaman makoki inda suka hallaka wani daga cikin masu jimami.

Kara karanta wannan

Najeriya ta tafka babban rashi: Tsohon mataimakin gwamna ya bar duniya

An shelanta mutuwar Christopher Igwe, dan'uwan kwamishina a gwamnatin Ebonyi bayan wasu ’yan fashi sun bude wuta.

Shaidu sun ce wannan lamari ya faru ne lokacin da mamacin da ’yan uwansa ke shirin tafiya addu'a na musamman, cewar Channels TV.

Yan bindiga sun yi barna a Ebonyi
Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi. Hoto: Hon. Francis Nwifuru.
Source: Facebook

An sace tsohon mataimakin gwamna

An ce maharan sun tilasta masa fitowa daga motarsa kafin su tafi da shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Shugaban karamar hukumar Ikwo, Sunday Nwankwo, ya tabbatar da sacewar, yana cewa hukumomi na hada kai da jami’an tsaro domin tattara bayanai.

Ya kara da cewa ana kokarin ganin an kubutar da shi cikin koshin lafiya ta hanyar hadin gwiwa da jami’an tsaro.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ebonyi, SP Joshua Ukandu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun bazu a yankin domin bin diddigin masu garkuwar tare da tabbatar da ceto dattijon lafiya.

Tsohon mataimakin gwamna ya rasu a Najeriya

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Delta ta fitar da wata sanarwa inda take jimami da tura sakon ta'aziyya bayan samun labarin mutuwar tsohon mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallata shi da shi a zaben 2027

Gwamna Sherrif ya bayyana rasuwar tsohon mataimakin gwamna a matsayin babban rashi ga jihar da kasa baki daya.

Marigayin ya taba zama mataimakin gwamna a lokacin mulkin James Ibori daga shekarar 1999 zuwa 2007 karkashin jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com