Gwamnatin Kano Ta Ja Kunnen Wasu Ƴan Kasuwa kan Karya da Gobarar Singer
- Gwamnatin Kano ta gargaɗi ‘yan kasuwar Singer kan sharara karya yayin da gwamnati ta fara duba yawan asarar da aka yi a gobara
- Kwamitin da gwamnati ta aika domin gane wa idanunsa da kididdiga asarar da aka yi a kasuwar ne ga yi gargadin
- Ya bayyana hukuncin da zai biyo baya matukar aka gano ɗan kasuwa ya sharara karya kan yawan asarar da ya tafka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗi ga ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a Kasuwar Singer da su guji gabatar da bayanan ƙarya domin cin gajiyar tallafin da ake rabawa.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana hakan ne bayan jagorantar kwamitin gwamnati zuwa wurin da gobarar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa 'yan kwamitin sun kai ziyarar gani da ido domin tattara alkaluma da ƙididdige yawan barnar da gobarar ta yi.
Kwamitin gwamnatin Kano ya ziyarci Singer
Da yake magana da manema labarai bayan duba ɓangarorin da gobarar ta shafa, SSG ya ce manufar ziyarar ita ce bai wa ƴan kwamitin damar ganin girman barnwr da idanunsu.
Umar Farouk Ibrahim ya ce:
"Babban dalilin zuwanmu wurin wannan ibtila’i biyu ne. Na farko shi ne mu ga da idanunmu yadda asarar dukiyoyi ta kasance a kasuwar.”
Umar Farouk Ibrahim ya bayyana barnar a matsayin mai yawa, yana mai cewa bayan rasa rai, irin wannan asara na daga cikin mafi muni da mutum zai iya fuskanta.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yi iya ƙoƙarinta wajen tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa, ko da yake ba za a iya mayar da abin da aka rasa gaba ɗaya ba.
Kwamitin gwamnati ya ja kunnen ƴan kasuwa
Kamitin ya kuma isar da saƙo ga ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a raba tallafin cikin gaskiya da adalci.
An ce an isar da saƙon ne ta hannun jami’an tsaro da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, ciki har da DSS, EFCC da ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda.

Source: Original
SSG ya jaddada cewa yan kwamitin mutane ne masu kima da mutunci, kuma ba za su kauce wa umarnin da aka ba su ba.
Umar Farouk Ibrahim ya gargadi duk wanda zai yi ƙoƙarin gabatar da ƙarya domin samun tallafi, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci rashin gaskiya ba.
Ya ce duk wanda aka kama yana ƙoƙarin karkatar da tallafin zai iya rasa duk wani tallafi da ya kamata ya samu, har ma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
A cewarsa, bai dace mutum ya ci moriyar wahalar wani ba. Ya ce idan ba za a taimaka wa masu buƙata ba, bai kamata a ribaci raɗaɗin su ba. Dangane da tallafi, ya ce Gwamnatin Tarayya ta bayar da Naira biliyan biyar yayin da Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC ta bayar da Naira biliyan uku.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Kwankwasiyya ta nuna yatsa ga Gwamna Abba kan zargin muzgunawa 'yan adawa
Haka kuma, an samu wasu kuɗi da suka kai miliyoyin Naira da aka bai wa ‘yan kasuwa kai tsaye yayin da aka yi asarar sama da N20m.
Yadda za a raba tallafin kasuwar Singer
A baya, kun ji cewa gwamnatin Kano ta kafa kwamitin mutane 23 domin raba tallafinNnaira biliyan takwas ga yan kasuwar Singer da gobara ta shafa.
Kwamitin zai tantance ainihin yan kasuwar da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an raba kudin cikin gaskiya da adalci domin a ragewa jama'a raɗaɗi da suka shiga.
Tallafin ya kunshi kudin da Shugaba Bola Tinubu da kungiyar gwamnonin APC suka bayar don farfado da tattalin arzikin yan kasuwar da iftila'in ya rutsa da su.
Asali: Legit.ng
