Ba Jira: Shugaba Tinubu Ya Yi Babban Tagomashi ga Shugaban NSCDC da Ya Ajiye Aiki

Ba Jira: Shugaba Tinubu Ya Yi Babban Tagomashi ga Shugaban NSCDC da Ya Ajiye Aiki

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cike gibin gurbin shugabanci da aka samu hukumar tsaro ta NSCDC
  • A ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026 shugaban hukumar NSCDC, Dr. Ahmed Abubakar Audi, ya ajiye aiki bayan kammala wa'adinsa
  • Sai dai, mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sake ba damar ci gaba da jagorancin hukumar NSCDC ga Dr. Ahmed Abubakar Audi

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa Dr. Ahmed Abubakar Audi a matsayin shugaban hukumar NSCDC na sabon wa’adin shekaru biyar.

Wannan sake naɗin da Shugaba Tinubu ya yi wa Ahmed Abubakar Audi ya fara aiki ne daga ranar Juma’a, 27 ga watan Fabrairu, 2026.

Shugaba Tinubu ya sabunta wa'adin a hukumar NSCDC
Dr. Ahmed Audi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Ba da jam'iyyu ba ne"; Atiku ya fadi masu fafatawa da Tinubu a zaben 2027

Tinubu ya sabunta wa'adin Audi a NSCDC

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Dr. Ahmed Audi a wannan matsayi a shekarar 2021.

Wa’adinsa na farko na shekaru biyar ya ƙare ne a ranar Juma’a da ta gabata, daidai lokacin da yake halartar shagulgulan bikin ranar jami’an tsaro ta farin kaya ta duniya a babban sakatariyar hukumar da ke Abuja.

Ana sa ran zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026.

Tinubu ya umurci Ahmed Audi da ya sake fasalin hukumar domin ta taka rawar gani sosai a harkar tsaron ƙasa, musamman a daidai lokacin da rundunar ’yan sanda ke mayar da hankali kan babban nauyin da ke kanta na kare ’yan ƙasa daga hannun ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da kuma ’yan ta’adda.

Wane ne Dr. Ahmed Audi?

An haifi Dr. Ahmed Audi a ranar 30 ga Satumba, 1967, a garin Laminga da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar NSCDC ya yi ritaya daga aiki, Tinubu zai maye gurbinsa

Bayan karatun firamare da sakandare a jihar, ya halarci kwalejin horar da malamai da ke Jengre a jihar Filato, inda ya samu takardar shaidar malanta ta mataki na biyu (Grade II) a shekarar 1987.

Ya ci gaba da karatu a Kwalejin Ilimi ta Akwanga (COE Akwanga), inda ya samu takardar shaidar NCE a shekarar 1992.

Sakamakon son da yake yi wa karatu, ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), inda ya kammala digirinsa na farko a fannin ilimin motsa jiki da kiwon lafiya a shekarar 1995.

Ya samu kwalaye a fannin karatu

A shekarar 2001, ya samu digiri na biyu a fannin gudanar da ayyukan gwamnati daga jami’ar Calabar.

Ya kuma samu digirin-digirgir (PhD) a fannin gudanar da ayyukan gwamnati daga jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi a shekarar 2014, sannan ya sake samun wani digirin na biyun a fannin tabbatar da doka da shari’ar manyan laifuffuka (MLCJ) daga Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 2019.

Tinubu ya sake nada Ahmed Audi a shugabancin hukumar NSCDC
Shugaban hukumar tsaro ta NSCDC, Dr. Ahmed Abubakar Audi Hoto: @Official_NSCDC
Source: Twitter

Yaushe Ahmed Audi ya fara aiki a NSCDC?

Dr. Ahmed Audi ya shiga hukumar NSCDC ne a watan Nuwamba, 1996, kuma aka tura shi matsayin jami’i mai kula da shiyya a ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa bayan ya kammala horon manyan jami’ai a shekarar 1997.

Kara karanta wannan

EFCC ta fito da Abubakar Malami, ta mayar da shi da iyalansa gaban kotu

Ya yi aiki a rassa daban-daban na jihohi, kuma a shekarar 2007 aka yi masa ƙarin girma zuwa matsayin Kwamanda, inda daga bisani aka tura shi ofishin babban kwamandan hukumar da ke babbar hedikwarta a Abuja.

An kori jami'ai daga hukumar NSCDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta kori wasu manyan jami'ai daga aiki a hukumar NSCDC.

Gwamnatin Tarayya ta kori manyan jami'ai 37 da wani mataimakin babban kwamanda (ACG) na hukumar NSCDC.

An kori ACG tare da wasu manyan jami’ai 37 saboda rashin biyayya da kuma halayen da ba su dace da manyan jami’ai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng