Halin da Khamenei da Shugaban Iran Ke Ciki bayan Hare Haren Amurka da Isra'ila

Halin da Khamenei da Shugaban Iran Ke Ciki bayan Hare Haren Amurka da Isra'ila

  • An shiga tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya bayan Amurka da Israila sun kaddamar da hare-haren kan Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
  • An kai hare-haren ne ta sama kuma wasu majiyoyi sun bayyana cewa manyan jami'an gwamnatin Iran na daga cikin wadanda ake so a kawar
  • Iran ba ta yi wata-wata ba, inda ta maida martani ta hanyar harba makamai masu linzami kan Isra'ila da sansanonin sojijin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Iran - Amurka da Isra'ila sun kai hare-haren hadin gwiwa kan kasar Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Daga cikin mutanen da hare-haren suka nufa har da Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, da kuma shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian.

Manyan jami'an gwamnatin Iran sun tsira a harin Amurka da Israila
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Ayatollah Ali Khamenei Hoto: @Khamenei, @drpezeshkian
Source: Twitter

Wata kafar yada labarai ta Isra'ila @kan_news ta rahoto cewa manyan jagororin na daga cikin mutanen da aka so hare-haren su kawar da su.

Kara karanta wannan

An rufe sararin samaniyar kasashe 8 da yaki ya barke tsakanin Iran da Amurka

An so farmakar jami'an gwamnatin Iran

Ta bayyana cewa wata majiya ta tabbatar da cewa hare-haren na da niyyar samun Ayatollah Ali Khamenei da Shugaba Masoud Pezeshkian.

“Jagoran Iran Khamenei da Shugaba Masoud Pezeshkian suna cikin jerin mutanen da harin ya nufa."

- Wata majiya

Wane jagororin Iran suke ciki?

Sai dai, tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa manyan jami’an gwamnati a Iran suna cikin “ƙoshin lafiya,”.

An bayyana cewa Shugaba Masoud Pezeshkian, shugaban majalisar dokoki Mohammad Bagher Ghalibaf, da kuma babban jami’in tsaro Ali Larijani.

Hakazalika, an bayyana cewa an dauke Ayatollah Ali Khamenei zuwa wani wuri mai tsaro.

“Yayin da majiyoyin Isra’ila suka yi iƙirarin cewa sun farmaki tare da yin nasarar kai hari ga shugaban ƙasa da manyan shugabannin Iran, majiyoyin hukuma a cikin ƙasar sun ba da rahoton cewa manyan jami’an gwamnati, ciki har da shugabannin dakarun soja, suna cikin ƙoshin lafiya."

- Wata majiya

Amurka da Israila sun so kashe Khamenei
Ayatollah Ali Khamenei tare da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Amurka da Isra'ila sun farmaki Iran

Kara karanta wannan

Iran ta kai hare hare Isra'ila, hayaki na tashi a sansanin sojin Amurka

Waɗannan hare-hare sun zo ne kwanaki biyu kacal bayan da aka kammala tattaunawar nukiliya tsakanin Amurka da Iran a birnin Geneva, wadda ƙasar Oman ta shiga tsakani, ba tare da an sami wata matsaya ba.

Wannan hari na Amurka da Isra’ila ya nuna mafi girman taƙaddama da aka samu tun bayan taƙaitaccen yaƙin da aka fafata mai tsanani a watan Yunin 2025.

Kasashen biyu dai na zargin Iran na kokarin mallakar makamin nukiliya, zargin da Iran ta dade tana musantawa.

Iran ta sha alwashin maida martani mai zafi kan hare-haren da kasashen biyu suka kai mata.

Iran ta harba makamai masu linzami

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kaddamar da gagarumin harin makami mai linzami kan sansanonin sojojin Amurka da ke a wasu manyan kasashen Gulf guda hudu.

Makaman Iran sun sauka a sansanonin sojojin Amurka a kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, Bahrain, da kuma Kuwait.

Hukumomi a kasar Bahrain sun tabbatar da cewa an harba makami mai linzami kan rundunar sojojin ruwan Amurka ta biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng