An Kama Wanda ke Tono Kabari Yana Cire Sassan Gawa a Watan Ramadan

An Kama Wanda ke Tono Kabari Yana Cire Sassan Gawa a Watan Ramadan

  • Rundunar 'yan sanda ta yi magana game da wani mutum da aka kama bisa zargin shiga makarbarta yana shirin tono gawa a kabari
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a kauyen Barwo Sabon Gari da ke wani yanki karamar hukumar Nafada a jihar Gombe
  • Wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da ake masa tambayoyi, ya kuma bayyana cewa ya tabo ciro sassan gawa a kabari a shekarar 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Asirin wani mutum mai suna Umar Ibrahim da abokan aikinsa ya tonu bayan shiga makabarta da niyyar tono gawa a kabari.

Legit Hausa ta gano cewa wani mutum mai suna Zakari Ibrahim ne ya ga wanda ake zargin a lokacin da ya shiga makabartar kuma daga nan ya sanar da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallata shi da shi a zaben 2027

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Mai sharhi kan lumuran yau da kullum da tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da ake yi masa tambayoyi.

An kama mai tonon kabari a Gombe

Majiyoyi sun shaida cewa a ranar 24, Fabrairu, 2026, wani mai suna Zakari Ibrahim mai shekaru 45, dan kauyen Barwo Sabon Gari, ya bayar da rahoton cewa ya ga Umar Ibrahim mai shekaru 30.

Zakari Ibrahim ya ce Umar Ibrahim da ya kasance mazaunin unguwar Madaki a gundumar Barwo Winde, yana tona wani kabari a makabartar Barwo Sabon Gari.

Biyo bayan rahoton ne hukumomin yankin suka kama wanda ake zargi domin gudanar da cikakken bincike a kansa da daukar mataki

Wanda ake zargi ya amsa laifinsa

A yayin bincike, an ruwaito cewa Umar Ibrahim ya amsa laifin cewa mahaifinsa, Ibrahim Usman mai shekaru 60, ne ya aike shi domin cire wasu sassan gawar mamaci don amfani da su wajen tsafi.

Kara karanta wannan

Firayim Ministan Birtaniya ya yi magana kan kama bature zai kai hari masallaci da gatari

Sai dai duk da amsa laifinsa, Umar Ibrahim ba bayyana hakikanin irin tsafin da suke yi da sassan gawa ba da kuma shekarun da ya shafe yana hakan.

Umar A Chuso a jihar Gombe
Kwamishinan 'yan sandan Gombe, Umar A Chuso. Hoto: Gombe State Police Command
Source: Facebook

Wanda ake zargi da tono kabari a 2025

Bugu da kari, Umar Ibrahim da ake zargi ya kara da cewa a shekarar 2025, ya taba tono yatsar kafar wani mamaci daga wannan makabartar.

Karin rahotanni sun nuna cewa bayan yanko sashen jikin gawar, ya mika ta ga wani mutum mai suna Alhaji Bappa Abdu mai shekaru 35, wanda shi ma daga yankin yake.

Wadanda 'yan sanda suka kama a Gombe

A halin yanzu, ‘yan sanda sun tabbatar da kama mutane ukun da ake zargi da alaka da laifin, kuma an ce sun amsa zargin laifuffukan da ake tuhumar su da aikatawa.

Rundunar ta kara da cewa bincike na cigaba da gudana, inda ake sa sa ran za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

'Yan Bauchi na gudun hijira a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa daruruwan jama'a a wasu kauyukan jihar Bauchi sun zama 'yan gudun hijira a jihar Gombe da wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Jami'in SS ya bindige wani da ya yi kokarin shiga gidan Trump da makami

Binciken Legit Hausa ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga hare-haren 'yan bindiga a kauyukan Gwana, Yalo, Digare da sauransu.

Gwamna Bala Mohammed ya ziyarci Gwana, inda ya bayyana cewa abin takaici ne yadda aka raba mutane da gidajensu, amma zai dauki mataki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng