Alkali Ya Dauki Muhimmin Mataki a Karar da Nasir El Rufai Ya Shigar gaban Kotu
- An samu tsaiko a karar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar domin neman kare hakkinsa na dan Adam
- Tsohon gwamnan dai na jihar Kaduna ya kasance a tsare tun bayan da ya kai kansa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC
- Alkalin kotun da Nasir El-Rufai ya shigar da kara a gabanta, ya mayar da fayil din shari'ar ga babbar alkalin kotun tarayya da ke Abuja
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dauki matsaya kan karar da Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar a gabanta.
Kotun ta mayar da fayil ɗin shari’ar neman kare haƙƙoƙin ɗan adam da tsohon gwamnan na Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shigar, zuwa hannun babban alƙalin babbar kotun tarayya ta Abuja domin sake mika shari'ar ga wani alƙalin daban.

Source: Twitter
Mai magana da yawun tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cikin wata sanarwa a shafinsa na X a ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026.
Alkali ya tafi hutu
Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da mai shari'a Belgore ya bayar a cikin kotun, inda ya bayyana cewa zai tafi hutu.
Sanarwarsa ta sa ta tafiya hutu ta sa ya zama dole a mayar da fayil ɗin shari’ar don a damƙa ta ga wani alƙali na daban.
Tun farko dai kotun ta ɗage sauraron wannan batu a ranar Laraba, 25 ga Fabrairu, zuwa ranar Alhamis domin sauraron neman belin da El-Rufai ya shigar.
Wannan ƙara dai tana neman kare haƙƙoƙin El-Rufai ne daga wasu hukumomin tsaro da na yaƙi da cin hanci da rashawa, waɗanda suka haɗa da Hukumar ICPC, EFCC, DSS, da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.
El-Rufai na ci gaba da zama a tsare
El-Rufai yana tsare ne tun ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, lokacin da ya kai kansa ofishin EFCC don amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.
Daga baya an mayar da shi zuwa hannun hukumar ICPC a daren 18 ga watan Fabrairun 2026.

Source: Twitter
Tsare El-Rufai da ake yi ya jawo martani daban-daban a faɗin ƙasar nan.
A ranar Laraba, shugaban kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola, ya buƙaci a gurfanar da El-Rufai a gaban kotu ko kuma a sake shi.
An yi zanga-zangar neman a binciki El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna, kan gwamnatin Nasir Ahmad El-Rufai da ta wuce.
Masu zanga-zangar sun buƙaci amsoshi kan ɓatan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, tare da yin kira ga a gudanar da bincike kan mulkin tsohon gwamna Nasir El-Rufai.
Sun yi kira da a fito fili a bayyana gaskiya game da bashin dala miliyan 350 da aka karɓo daga Bankin Duniya a zamanin tsohon gwamnan.
Asali: Legit.ng
