Masu Mu'uzijar Karya: An Cafke Malaman Addini 6 da Ke Damfarar Mutane a Najeriya

Masu Mu'uzijar Karya: An Cafke Malaman Addini 6 da Ke Damfarar Mutane a Najeriya

  • 'Yan sanda sun kama wasu mutane shida a Jihar Ondo wadanda suka yi sojan gona a matsayin fastoci domin damfarar mutane
  • Wadanda ake zargin sun yi amfani da mu'ujizoji na karya don yaudarar mutane ta hanyar cewa suna magance matsalolin kudi da lafiya
  • Rundunar yan sandan ta gargadi jama'a da su kiyayi mutanen da ke tallata mu'ujizoji da sunan malaman addini ne don aikata damfara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ondo - Rundunar ƴan sandan Jihar Ondo ta sanar da kama wasu mutane shida waɗanda ake zargi da damfarar mazauna yankin Idanre ta hanyar nuna kansu a matsayin fastoci.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Jimoh Kazeem, ya bayyana cewa waɗanda ake zargi sun yi amfani "mu'ujizoji na ƙarya" domin yaudarar mutanen da ba su san komai kan addini ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta saki hotunan wasu manyan ma'aikatan gwamnati da ake zargi da zambar N2bn

'Yan sanda sun kama fastoci 6 da ke karyar mu'uzija don su damfari mutane.
Cikin ginin wata coci, lokacin da babu mutane a ciki. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

'Yan sanda sun kama fastocin bogi

Waɗanda aka kama sun haɗa da Fadahunsi, Kolade, Tijani, Iyanuoluwa, Arijesulola, da kuma Ademola, in ji rahoton jaridar Punch.

Jami'an rundunar tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron COS ne suka kai samamen da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin a ranar 16 ga watan Fabrairu.

"A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, jami'an sashen CTT na rundunar 'yan sanda tare da hadin gwiwar jami'an tsaron CSO suka kaddamar da wani samame mai cike da nasara, bayan samun sahihan bayanan sirri na ayyukan wasu mutane da ke damfarar mutane a Idanre da kewaye."

- Jimoh Kazeem.

Yadda fastocin bogi ke damfarar mutane

Binciken farko ya nuna cewa mutanen sun tsara damfarar ne ta hanyar da za su samu amincewar mutane, inda suka rika nuna cewa suna da ikon magance matsalolin rayuwar yau da kullum.

Jimoh Kazeem ya bayyana cewa:

"Sun yi amfani da raunin zukatan mutane ta hanyar yi musu alkawarin mafita ga matsalolin kuɗi da na lafiya domin su damfare su."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki wurin ibada a watan azumi, sun bude wa mutane wuta

'Yan sandan sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun tsara komai a tsakaninsu, inda kowanne aka raba masa aikin da zai rika yi domin nuna cewa su fastoci ne na gaske.

'Yan sanda sun ce za su gurfanar da wadanda ake zargi da zararan kammala bincike
Taswirar jihar Ondo, inda aka kama fastocin bogi suna damfarar mutane. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Za a gurfanar da fastocin bogi

A halin yanzu, ana ci gaba da bincike domin gano yawan kuɗaɗen da suka damfara da kuma sauran mutanen da suka taimaka musu wajen wannan aika aika.

Rundunar ta buƙaci jama'a da su kasance masu taka-tsantsan tare da guje wa mutanen da ke amfani da addini ko mu'ujizoji domin aikata miyagun ayyuka.

Dukkan waɗanda ake zargin suna tsare a hannun ƴan sanda kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zaran an kammala bincike,a cewar sanarwar.

An fallasa fasto mai mu'ujizar karya

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata daliba ta kwancewa fasto zani a soshiyal midiya kan kin bata cikon N100,000 bayan ta yi karyar kurumta a wani shirin mu'ujizar bogi.

Kamar yadda dalibar ta bayyana, faston ya biya ta N100,000 a matsayin somin tabi domin ta yi karyar kurumta, tare da alkawarin cika mata N100,000 bayan gama shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com