Asiri ya tonu: Yadda aka kama fastoci biyu sunyi amfani da mace daya wajen nuna mu'ujizar karya (Bidiyo)
- Asirin wasu fastoci ya tonu, bayan an kama su suna amfani da wata mata wajen bayyana mu'ujizar karya
- An gano fastocin a wasu bidiyoyi guda biyu a wurare mabanbanta suna amfani da matar
- Matar dai ta nuna hannunta ya shanye ne inda su kuma fastocin za su yi mata addu'a sai hannun ya koma daidai
Wani bidiyo da yake nuni da wasu fastoci guda biyu suna amfani da wata mace a lokacin da suke bayyana mu'ujizarsu ta karya ya karade kafafen sada zumunta.
A duka bidiyoyin guda biyun wanda suke da fastoci daban-daban a kuma wuraren bauta daban-daban, hannun matar wanda yake shanyayye ne ya dawo ya daidai bayan fastocin sun yi mata addu'a.
An riga an bankado daya daga cikin fastocin mai suna Fasto Chris Okafor wanda yake jagorantar babbar cocin 'Mountain of Liberation and Miracle'.
KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Budurwa ta bayyana yadda ta tsinci kanta tana zina da kare
Yanzu haka dai mutane na ta faman bincike domin gano dayan fasto dake cikin dayan bidiyon domin bayyana kowanene shima a shafukan sadarwa.
A Afrika dai musamman Najeriya fastoci suna cin karen su babu babbaka a wajen mabiyan su, inda suke yi musu karyar suna da wata baiwa amma fa ta karya. Bayan haka kuma an sha kama fastocin dumu-dumu suna aikata zina da mambobin su mata na coci, banda wasu da ake kamawa da laifin garkuwa ko kuma wasu abubuwa na ta'addanci makamantan haka.
Ga dai bidiyon fastocin a kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng