Garambawul: Gwamna Ya Nada Sabon Shugaban Ma'aikata da Sakataren Gwamnatin Jiha

Garambawul: Gwamna Ya Nada Sabon Shugaban Ma'aikata da Sakataren Gwamnatin Jiha

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya nada sabon sakataren gwamnati da kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Rivers
  • Wadannan sababbin nade-nade sun biyo bayan sulhun da Shugaba Bola Tinubu ya yi tsakanin gwamnan da ministan Abuja
  • Tun bayan rikicin siyasa da ta barke a jihar Rivers ake takaddama kan mukamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya naɗa Dr. Dagogo S.A. Wokoma a matsayin sabon sakataren gwamnatin jiha (SSG).

Haka kuma, gwamnan ya nada lauya, Sunny Ewule a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Rivers.

Gwamna Siminalayi Fubara ya nada sabon sakataren gwamnati da shugaban ma'aikata.
Gwamna Siminalyi Fubara ya na jawabi a bikin ranar Eneka da aka gudanar a Fatakwal. Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Twitter

Rivers: Gwamna ya yi sababbin nade nade

Sanarwar ta fito ne a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026, ta hannun babban sakataren yaɗa labarai na gwamna, Onwuka Nzeshi, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gobara: Matakan da gwamnatin Kano za ta bi wajen raba N8bn ga ƴan kasuwar Singer

Wannan mataki dai ya nuna cewa naɗin ya fara aiki ne nan take, inda aka rantsar da su da misalin ƙarfe 2:00 na ranar yau a fadar gwamnati da ke Fatakwal.

Naɗin sabon sakataren gwamnatin na nufin Dr. Wokoma ya maye gurbin Mista Benibo Anabraba, yayin da Mista Sunny Ewule ya maye gurbin Edison Ehie.

Tasirin sulhun Tinubu a siyasar Rivers

Matsayin Edison Ehie ya kasance abin taƙaddama tun bayan rikicin siyasa da ya faru a jihar, kodayake wasu majiyoyi sun ce yana gudanar da aikin ne a asirce.

Gwamnatin ba ta bayar da wani takamaiman dalilin cire tsofaffin jami'an ba, sai dai ana kallon hakan a matsayin matakin share fage ga sabuwar tafiyar sulhu, in ji rahoton Punch.

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun yi amanna cewa waɗannan naɗe-naɗe sakamako ne na sasancin da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta tsakanin Gwamna Fubara da tsohon ubangidansa, Ministan Abuja Nyesom Wike.

Gwamna Fubara ya bukaci sababbin jami'an gwamnatin jihar Rivers su yi aiki cikin gaskiya
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara yana sanya hannu kan wata takarda a fadar gwamnatin Rivers. Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Facebook

Garambawul a gwamnatin jihar Rivers

A baya bayan nan, majalisar dokokin Rivers, ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule, ta janye ƙudurin tsige gwamnan da mataimakiyarsa sakamakon wannan sulhu yanzu.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince da nadin malamin addini a matsayin mataimakin gwamna a Najeriya

Gwamna Fubara ya riga ya rushe dukkan majalisar zartarwar jihar da masu ba shi shawara na musamman kwanakin baya domin kafa sabuwar gwamnati.

Wannan canji na muƙaman sakataren gwamnati da Shugaban Ma'aikata ana kallonsa a matsayin babban mataki na farko wajen dawo da zaman lafiya da haɗin kai a siyasar Jihar Rivers yanzu.

Rigima a Rivers kan nadin mukamai

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata sabuwar takaddama na kunno kai tsakanin bangaren Gwamna Siminalayi Fubara, da na Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rigimar ta kunno kai ne kan wasu muhimman bangarori na yarjejeniyar sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani ya cimma watanni da suka gabata.

Fubara dai ya rike kwamishinoni takwas da hukuncin Kotun Koli bai shafe su ba, bayan ya rushe majalisar zartarwa da dokar ta-baci ta kare, lamarin da majalisa taki yarda shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com