Malami Ya Gargadi Mata Kiristoci kan Auren Musulmi, Ya Fadi Illar da ke Ciki

Malami Ya Gargadi Mata Kiristoci kan Auren Musulmi, Ya Fadi Illar da ke Ciki

  • Malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi magana game da mata Kiristoci da ke auren mazaje wadanda suke da addini daban-daban
  • Emmanuel Iren ya gargadi mata Kirista kan auren Musulmi, yana cewa dole ne a fifita daidaiton bangaskiya fiye da soyayya
  • Wannan malami ya ce aure tsari ne na Allah, kuma Littafi Mai Tsarki ya hana auren wadanda ba su da addini iri daya da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babban Fasto kuma wanda ya kafa cocin 'Celebration International', Emmanuel Iren, ya gargadi Kiristoci kan auren Musulmi.

Faston ya shawarci mata Kirista da su guji auren Musulmi, yana mai cewa daidaiton bangaskiya cikin Almasihu ya fi muhimmanci fiye da soyayya ko jin dadi.

Fasto ya gargadi mata Kiristoci kan auren Musulmi
Fasto Emmanuel Iren yayin da yake huduba a coci. Hoto: @pst_iren/James Wakibia/SOPA Images/LightRocket.
Source: UGC

A wani bidiyo da ya yadu wanda Tribune ta samu, Faston ya amsa tambayar wata mata da ta nemi shawara kan dangantakarta da wani saurayi Musulmi.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Oluremi Tinubu ta tuna yadda Musulman Arewa suka kare ta

Budurwa ta nemi shawara kan auren Musulmi

Matar ta bayyana cewa saurayin nata ba mai tsananin riko da addini ba ne, kuma ba ya adawa da Kiristancinta, har ma yana karfafa mata gwiwa wajen kusantar Allah.

Sai dai ta ce iyayenta ba sa son Musulmi kwata-kwata, kuma ta taso ne a gidan da ya tarwatse, mahaifinta fasto ne, lamarin da ya sa take tsoron yin auren da babu cikakkiyar goyon bayansu.

Ta ce:

“Ina da saurayi Musulmi, amma ba mai tsananin riko da addinin Musulunci ba ne. Ba ya adawa da addinina. Yana karfafa ni in kyautata rayuwata kuma in kusanci Allah.
"Yana da halaye da siffofin da nake so, kuma ina ganinsa a matsayin wanda zan aura. Amma iyayena ba sa son Musulmi kwata-kwata. Ni ma na taso a gidan da iyaye suka rabu, kuma mahaifina fasto ne.
"Na san yadda yake idan mutum ya auri wanda ba a kaunarsa ko girmama shi a gida kawai saboda dalilin addini. Shekara daya kenan muna tare; shin in rabu da shi?”

Kara karanta wannan

Najeriya ta cire tsoro ta karyata rahoton Amurka kan Kiristoci

Fasto ya fadi hatsarin dake cikin Kirista ta auri Musulmi
Matashin Fasto a Najeriya, Emmanuel Iren. Hoto: @pst_iren.
Source: Instagram

Gargadin da Faston ya yi wa budurwar

A martaninsa, Fasto Iren ya ce kamar yadda ba za ka shiga gidan haya ka sauya tsarinsa ba, haka ma aure tsari ne da Allah Ya tsara, dole a bi ka’idarsa.

Ya ambaci umarnin Littafi Mai Tsarki na kada a daura aure da wanda ba ya cikin addininku, yana mai cewa Kiristoci bai kamata su shiga auren da ya saba wa gaskiyarsu ba.

Faston ya kuma bayar da labarin wata mata a Abuja da ta auri Musulmi da ta dauka mutum ne nagari kuma mai girmama addininta, amma bayan aure ya hana ta zuwa coci, har ma ya saka wa dansu da sunan Musulunci tare da hana shi zuwa coci.

Ya ce ko da yake ba duk irin wadannan aure ne ke karewa haka ba, amma ya gargadi mata da su fifita manufar Allah a aure fiye da jin dadi, yana cewa gida mai tushe cikin Almasihu ya fi muhimmanci fiye da soyayya kadai.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Plateau: Gwamna ya ba da umarni bayan tsoron barkewar rikici

Fasto ya yi hasashen garambawul a gwamnatin Tinubu

An ji cewa Fasto Elijiah Ayodele ya yi hasashe game da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu zai yi manyan sauye-sauye kafin karshen 2026.

Faston ya ce sauyin shugabannin tsaro na da nasaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027 da ake tunkara a Najeriya.

Malamin ya gargadi shugabannin tsaro su shirya, yana mai cewa hukuncin ya riga ya tabbata sai dai idan Allah ya sauya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.