Gwamnatin Abba Ta Yi Martani Mai Zafi kan Zargin Cin Zarafin 'Yan Adawa
- Kungiyar Amnesty International ta jefi gwamnatin jihar Kano da zargin cin zarafin 'yan adawa masu sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Gwamnatin jihar Kano ta fito ta yi martani kan zargin da ake yi mata na kamawa tare da tsare masu caccakar gwamnan
- Ta bayyana cewa akwai bambanci tsakanin fadar albarkacin baki da kuma bata suna da yada labaran karya da karairayi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan zargin cin zarafin 'yan adawa da ke sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin ta yi watsi da zarge-zargen da ƙungiyar Amnesty International ta yi na cewa ita ce ke kamawa, tsarewa, da cin zarafin mutanen da ke sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al'amuran cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Kwankwasiyya ta nuna yatsa ga Gwamna Abba kan zargin muzgunawa 'yan adawa
Amnesty ta yi zargi kan Gwamnatin Kano
Kungiyar Amnesty International ta zargi hukumar DSS da kasancewa kan gaba wajen wannan danniya, inda ta ce galibi ana “gayyata” ko tsare ’yan ƙasa waɗanda laifinsu kawai shi ne bayyana ra’ayoyin da suka saɓa wa na gwamnan.
A cewar Amnesty, wannan yanayi yana haifar da tsoro da kuma takura wa ’yancin gudanar da harkokin jama’a a jihar.
Wane martani Gwamnatin Kano ta yi?
Sai dai a cikin sanarwar, Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba daidai yake ba, mara tushe, da kuma karkatar da gaskiya.
A cewar sanarwar, gwamnatin Gwamna Abba tana nan kan bakanta wajen kare haƙƙoƙin ɗan adam, har da ’yancin faɗar albarkacin baki, amma ta jaddada cewa irin waɗannan haƙƙoƙin suna da iyaka.
Ta bayyana cewa ɓatanci, cin mutunci, kalaman kiyayya, tunzurawa, da gangancin yaɗa labaran ƙarya ba sa cikin rukunin ’yancin faɗar albarkacin baki da doka ke ba kariya.
"Babu wata al’ummar dimokuraɗiyya da za ta amince da mayar da kafafen sada zumunta makamin yaƙi domin yaɗa ƙaryar da za ta ɓata suna ko kuma wani abin da zai iya dagula zaman lafiyar jama’a da sunan yin amfani da ’yancin faɗar albarkacin baki.”
- Ibrahim Abdullahi Waiya
'Hukumomin tsaro ke aikinsu' - Kwamishinan labarai
Kwamishinan ya ƙara bayyana cewa hukumomin tsaro, ciki har da DSS, suna aiki ne kawai a cikin tsarin dokokin da suka kafa su.
Ya ce kamawa ko gayyatar mutane yana dogara ne kan korafe-korafe ko zarge-zarge masu tushe na aikata ba daidai ba kamar cin zarafi a intanet, ɓata suna, ko tunzurawa.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatın jihar Kano ba ta juya ko sarrafa hukumomin tsaro na tarayya, amma tana goyon bayan ƙoƙarinsu na yaƙi da laifuffukan intanet da kuma kare mutuncin ’yan ƙasa.

Source: Facebook
Gwamnati ta musanta zancen cin zarafin 'yan adawa
Ya jaddada cewa jama'a na da ’yancin bayyana ra’ayoyinsu kan shugabanci ba tare da cin zarafi ba, amma ta yi gargaɗin cewa akwai iyaka tsakanin suka da ɓata suna, sannan akwai bambanci tsakanin adawa da tunzurawa.
“Gwamnatın jihar Kano ba ta cin zarafin masu fada a ji a kafafen sada zumunta ko abokan hamayyar siyasa."
- Ibrahim Abdullahi Waiya
Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta umurci a rufe makarantu don hutun Sallah.
Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta ayyana ranar Lahadi, 1 ga watan Maris, 2026, a matsayin ranar da za a fara hutun ƙaramar Sallah.
Hutun ya shafi dukkanin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da ke a fadin jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

