Wani Ya Shigo Masallaci da Makami Tsirara, Masallata 5000 Sun Fice ana Azumi
- Wani mutumi dauke da makami ya shiga babban masallacin birnin Manchester da ke kasar Birtaniya mai daukar musulmai sama da 5,000
- Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata amma tuni yan sanda suka kama shi tare da kaddamar da bincike kan lamarin
- Kwamitin Masallacin ya bayyana cewa mutane biyu aka gani da alamun zargi, an kama daya amma dayan ya gudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Manchester, England - ’Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 40 bayan da aka yi zargin ya shiga Babban Masallacin birnin Manchester da ke kasar Burtaniya dauke da makami a daren ranar Talata.
An kira jami'an tsaro zuwa masallacin da ke yankin Victoria Park a birnin da misalin karfe 8:40 na dare, bayan an fara zargin wasu mutane biyu da suka shiga masallacin.

Source: Getty Images
Tribune Nigeria ta ce ’yan sanda sun isa wurin kuma sun kama wanda ake zargin guda daya, wanda har yanzu yana tsare.
Wani mutumi ya shiga masallaci da makami
An ce mutum na biyun kuma bai shiga hannu ba, inda jami'an tsaro ke neman bayanan da za su kai ga kamo shi.
Wani shaida ya bayyana cewa wanda ake zargin, wanda shekarunsa suka haura 40, ya shiga masallacin ne dauke da gatari.
"Mutane hudu ne suka danne shi tare da bugunsa da abin kashe gobara," in ji shi.
Ya kara da cewa an bukaci masallata kusan 5,000 da su fice daga masallacin, sannan motocin ’yan sanda kusan 15 ne suka isa wurin, amma babu wanda ya ji ko da kwarzane.
Matakin da yan sanda suka dauka
Sufeto Simon Nasim, na yankin Manchester, ya ce:
"A yammacin jiya, jami’ai sun ziyarci wani masallaci bayan samun rahoton wasu maza biyu sun yi alamun zargi, sannan suna dauke da makami mai hadari a lokacin da mutane ke tsaka da ibada a cikin wannan watan mai alfarma na Ramadan.

Kara karanta wannan
Bincike ya tono ministan Buhari da wani mutum sun fitar da miliyoyi a kifar da Tinubu
“Mun yi gaggawar kama mutum daya, kuma jami’ai suna aiki don gano mutum na biyun. Babu wata barazana, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya ji rauni.
“Za ku ga karuwar sintiri a yankin yayin da muke ci gaba da bincike. Don Allah ku saki jiki ku tattauna da jami’anmu tare da sanar da su damuwar da kuke da ita,” in ji Nasim.
A cikin wata sanarwa, kwamitin masallacin ya ce wasu mutane sun lura da wata jaka da ake zargi, inda suka raka daya daga cikin mutanen zuwa wani daki na daban.

Source: Getty Images
Kwamitin masallaci ya fitar da sanarwa
Sanarwar ta kara da cewa:
"An mika dukkan bayanan da suka dace da bidiyon kyamarar tsaro (CCTV) ga ’yan sanda wadanda ke ci gaba da bincike.
“Al’ummar Musulmi a Birtaniya suna fuskantar karuwar barazana da kiyayya a baya-bayan nan. Karuwar kyamar Musulunci abin damuwa ne sosai. Za mu ci gaba da ba da cikakken hadin kai ga ’yan sanda.
Wannan lamari ya faru ne mako guda bayan fara azumin Ramadan, kuma saura kwana daya kafin mutanen kudancin Greater Manchester su yi zaben cike gurbi na Gorton da Denton.
'Dan bindiga ya bude wa limami wuta a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa wani dan bindiga ya bude wa motar Imam Shuaib wuta a jihar Utah ta kasar Amurka yayin da aka fara azumin Ramadan.
Jami'an ƴan sandan Sandy sun tabbatar da cewa maharin ya yi harbi sosai a kan motar limamin lokacin da ya tsaya a kusa da motarsa.
Imam Shuaib ya bayyana cewa mutumin ya fito ne daga cikin mota, sannan ya buɗe masa wuta amma cikin ikon Allah bai raunata ba.
Asali: Legit.ng

