Manyan Jami'a 29 da za Su Yi Ritayar Dole bayan Sufeton Yan Sanda Ya Yi Ritaya
- Ritayar da tsohon Sufeton yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi za ta jawo sauye-sauye da dama a rundunar
- Bayan Shugaban kasa ya nada AIG Olatunji Disu a matsayin sabon Sufeton yan sanda, dole wasu manyan jami'ai su ajiye aiki
- Ana sa ran za a yi babban garambawul a manyan mukaman rundunar ‘yan sandan Najeriya yayin da aka gano wanda za su tafi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – A ranar Talata, 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2026 ne aka samu labarin cewa Sufeto janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya ajiye aiki.
Tun bayan ajiye aikin da babban jami'in ya yi, aka fara samun manyan sauye-sauye a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa yanzu haka, ana sa ran murabus din zai haifar da ritayar dole ga akalla mataimakan Sufeto Janar (DIG) takwas.
Ana samun sauyi a rundunar 'yan sandan Najeriya
Vanguard ta wallafa cewa sauyin na zuwa ne bayan nadin Mataimakin Sufeto Janar (AIG), Olatunji Disu, a matsayin sabon Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (IGP).
Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa akalla DIG hudu za su yi ritaya tare da Egbetokun a wani bangare na sauyin shugabanci da aka saba gani idan aka samu sabon IGP.

Source: Facebook
Masu ruwa da tsaki a rundunar sun ce irin wannan sauyi na faruwa ne musamman idan sabon IGP ya fi wasu manyan jami’ai karancin matsayi a jerin girma, ko kuma wasu daga cikinsu sun kusa cika ka’idar shekarun ritaya.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko DIG Fayoade Adegoke, DIG Funsho Adegboye da DIG Mohammed Adamu Dankwara, wadanda aka kara musu girma kwanan nan, su ma za su yi ritaya ba.
Manyan 'yan sandan da za su iya ritaya
Wani jerin sunaye da ke yawo a cikin rundunar ta nuna cewa shugabannin wasu muhimman sassa na iya yin murabus.
Daga cikin su akwai DIG Yahaya Abubakar, DIG Adebola Hamzat, DIG Adebowale Williams, DIG Sadiq Idris Abubakar, DIG Ben Nebolisa Okolo da DIG Basil Idegwu.
Wani AIG da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa ficewar wasu DIG abu ne da aka saba gani idan aka daga mukamin jami’i da ya fi su kankanta zuwa matsayin IGP.
A cewarsa, rundunar na da tsayayyen tsarin girma, wanda ke nufin idan aka nada jami’i da akwai manya a gabansa, ana bukatar manyan da ke sama da shi su yi ritaya.
Ya kara da cewa uku daga cikin sababbin DIG da aka kara wa mukami na iya yin ritaya tsakanin watan Yuni da Yuli saboda cika shekarun aiki ko shekaru a hidima.
Sufeton 'yan sanda ya yi ritaya
A baya, mun wallafa cewa rahotanni daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya umarci Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya ya yi murabus.
Majiyoyi daga hedkwatar rundunar yan sanda sun tabbatar da lamarin, kuma tuni aka nada wanda zai wakilci Kayode Egbetokun domin a ci gaba da aiki.
Rahotanni sun nuna cewa Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya (IGP) ya yi murabus daga mukaminsa ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

