Najeriya Ta Rasa Mahaddacin Kur'ani a Madina, Shugaban Gwamnoni Ya Yi Ta'aziyya

Najeriya Ta Rasa Mahaddacin Kur'ani a Madina, Shugaban Gwamnoni Ya Yi Ta'aziyya

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya yi ta'aziyyar rasuwar wani dalibin Kur'ani dan Najeriya a jami'ar Musulunci ta Madina
  • Dalibin mai suna Usama Ahmad Musa ya rasu bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita a kasa mai tsarki bayan 'yan shekaru yana karatu a can
  • Sheikh Isa Ali Pantami ya isar da sakon ta'aziyya daga Abuja, yayin da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ziyarci gidansu marigayin a Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Ana cigaba da jimamin rasuwar mahaddacin Al-Qur'ani, Usama Ahmad Musa da ya rasu a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.

Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar Usama.

Usama Ahmad Musa da Gwamna Inuwa Yahaya
Usama Ahmad Musa a hagu Gwamna Inuwa Yahaya a dama. Hoto: Abdallah Umar Dokaji|Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Mai magana da ya yawun gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya wallafa a Facebook cewa dalibin ya rasu yana da shekara 26 a duniya.

Kara karanta wannan

Sheikh Murtala Asada ya yi fatali da neman yafiyar Tinubu, ya jero dalilansa

Ta'aziyyar gwamna Inuwa Yahaya

Gwamna Inuwa ya bayyana rasuwar a matsayin rashi mai raɗaɗi da babbar hasara ga iyalansa, al’ummar Musulmi da kuma jihar Gombe baki ɗaya.

Sanarwar gwamnati ta ce Usama ɗa ne ga limamin Masallacin Chikaire da ke Gombe,Sheikh Ahmad Musa kuma an san shi a matsayin mai himma wajen neman ilimin addini, wanda ya kasance mai tawali’u, ladabi da jajircewa wajen karatu.

Gwamnan ya kuma bayyana shi a matsayin matashi mai sauƙin kai, mai mayar da hankali kan abin da ya sa gaba, mai tsoron Allah, wanda sha’awarsa ga neman ilimi da kyawawan halayensa suka bambanta shi a tsakanin takwarorinsa.

Inuwa Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, ’yan uwa, abokan karatu da daukacin al’ummar Musulmi, yana addu’ar Allah Maɗaukaki cikin rahamarsa mara iyaka Ya yafe masa kura-kuransa.

Maganar Daurawa da Pantami

A daya bangaren, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayi Usama Ahmad Musa, inda ya ce babban rashi ne ga al'ummar Musulmi.

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Pantami ya ce sama da shekara 30 da suka wuce ya san mahaifin marigayin a matsayin mahaddacin Kur'ani.

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami yayin wa'azi a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Sheikh Aminu Daurawa da ya isa jihar Gombe tafsiri, ya je gidan mahaifin marigayin domin yi masa ta'aziyya, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A bayanin da ya yi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa Manzon Allah SAW da kansa ya rasa 'ya'ya, saboda haka ya ya bukaci mahaifin marigayin ya yi hakuri.

Inuwa ya ba Daurawa gida a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa katafaren gida.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa gwamna Inuwa Yahaya ya kira shi a waya ya sanar da shi cewa ya gina masa masaukin da zai rika zama idan ya zo tafsir jihar.

A lokacin tasiri, malamin ya sanar da cewa an kammala komai a gidan, inda ya ce an saka gado da katifa, an yi madafi, an saka kujeru, sola da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng